Najeriya: Matsalar karancin takardar kudi ta sake kuno kai
November 10, 2023Bakon da aka rabu da shi ne dai ya nemi dawowa a Najeriyar inda bayan samun sauki da ma fara mancewa da wannan matsala da ta jefa ‘yan Najeriyar cikin mawuyacin hali. Karancin kudi da aka danganta shi da wa'adin da a can baya aka bayar na kin barin karbar takardun kudi Naira N1000da N500 da kumas N200. Na zagaya domin jin halin da ake cikin a kan wannan lamari. Wasu ‘yan kasar dai sun fara kin karbar takardun kudin ne da aka samar da sababi a madadinsu amma kotu ta tilasta wa babban bankin a wancan lokaci ya tsawaita wa'adin amfani da su har zuwa watan Disambar wannan shekara.
Wacce illa kin karbar takardar kudin ke yi ga tattalin arzikin Najeriya?
Karancin takardun kudi dai babbar matsala ce ga harkokin cinikaiyya a Najeriya, kasar da duk da bullo da tsarin cinikaiyya ba tare da kudi a hannu ba har yanzu ake dogara sosai wajen mu'amala da takardun kudi a hannu. Amma wace illa kin karbara takardar kudi ke yi ga tattalin arziki? Alhaji Shuaibu Idris Mikati masanin tattalin arziki da ke Najeriyar ya ce ya kamata babban banki Najeriya ya dau mataki a kai. Tuni dai babban bankin Najeriya ya hanzarta fitar da sanarwar a kan lamarin, inda ya bayyana cewa babu batun wancan wa'adi da ake magana don haka a ciki gaba da karbar kudadden. Sanarwar da ta samu sa hannun daraktan yada labaru na bankin Ambdulmumini Isa ta samar da sauki. ‘Yan Najeriya dai sun razana da sake kuno kan wannan matsala domin sai da kotun kolin Najeriya ta shiga lamarin a ranar 3 ga watan Maris din da ya gaba ne, ta tilasa wa babban bakin tsawaita lokacin .