1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar tsagerun Niger Delta ga Najeriya

Muhammad Bello ZUD/ZMA
November 8, 2022

A Najeriya, tsagerun yankin Niger Delta na barazanar komawa ruwa madamar gwamnati ba ta janye aniyarta ta kawo karshen shirin afuwar da ya dakatar da su daga fasa bututun mai ba.

https://p.dw.com/p/4JDz3
Tsagerun kungiyar MEND wacce a baya ta yi yaki da gwamnatin Najeriya
Tsagerun kungiyar MEND wacce a baya ta yi yaki da gwamnatin NajeriyaHoto: picture-alliance/dpa/G. Esiri

Wasu bayanai a baya daga gwamnatin Najeriya ne dai suka nuna da cewar jagoran shirin na Amnesty ya karbi umurni daga fadar shugaban kasa na shirya kawo karshen shirin na afuwar tsagerun na Niger Delta bayan shekaru 13 da aka kwashe ana aiwatar da shi.

Tun lokacin da labarin ya fara karade shafukan sada zumunta sai  kungiyoyin tsaffin tsagerun da ke sansanoni dabam-dabam suka fara barazanar za su koma cikin surkukin ruwayen yankin don fara dawo da hare-haren da suka saba a kan bututun mai da suaran kayan aiki na kamfanonin hakar man.

A zamanin da ayyukan tsaffin tsagerun ke kan ganiyarsa, hare-haren da suka yi ya sababba mayar da Najeriya komawa hako ganguna mai 700,000 kacal a rana, a maimakon ganguna kusan miliyan biyu da kasar ke hakowa a duk rana a tsakanin shekarun 2015 zuwa 2017.

Madam Ankio Briggs, mamba ce a kungiyar dattawan yankin ta PANDEF ta kuma ce yau kusan shekaru sha biyu ko fiye da kaddamar da shirin na afuwa, amma har yanzu su ba suu ga amfanin da suke tsammani ba, saboda ba shiri ba ne na raya kasa. Ta yi zargin shiri ne kawai na wasu tsurarun matasa da janye shi ka iya haifar da karuwar tashin hankali a yankin.

Jagoran aiwatar da shirin na afuwa a Niger Delta janar Barry Ndiomu mai murabus ya kwantar da hankulan tsagerun da ke kokarin komawa ruwa a sakamakon yunkurin da gwamnati ta yi na rufe shirin afuwar. A yanzu ya ce zai tabbatar nan ba da jimawa ba tsagerun da ke cikin shirin sun samu alawus din da gwamnati ke ba su a kowane wata.

Kungiyoyin tsagerun dai sun hada da Niger Delta Volunteer Force ta su Asari Dokubo da Niger Delta Vigilante ta su Ateke Tom da yanzu ya zama babban Sarki mai daraja ta daya a yankin. Akwai kuma kungiyar MEND ta su Tompolo da yanzu gwamnati ta ba shi kwangilar biliyoyin nairori ta tsaron bututayen mai.