1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsawaita dokar ta-baci a Borno da Yobe da Adamawa

Ubale MusaNovember 17, 2014

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta mikawa majalisar dokoki bukatar tsawaita dokar ta-baci a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa da nufin cigaba da yaki da 'yan Boko Haram.

https://p.dw.com/p/1DotD
Nigeria Boko Haram Terrorist
Hoto: picture alliance/AP Photo

Wannan yunkuri na gwamnatin ta Najeriya dai wanda shi ne irinsa na uku na zuwa ne kwanaki kalilan kafin karewar wa'adin watanni shidda na wannan doka da aka tsawaita a farkon wannan shekarar a jihohin na Borno da Yobe da Adamawa.

Verletzte nach dem Anschlag in Potiskum Nigeria 10.11.2014
Hare-haren Boko Haram na cigaba da hallaka mutane da jikkata wasu da damaHoto: picture-alliance/Ap Photo/A. Adamu

Majalisar tsaron Najeriya ce dai ta gudanar da wani taro a fadar babban birnin kasar Abuja a ranar Litinin inda ta ce ta ga dacewar tsawaita dokar domin cigaba da yakar 'yan kungiyar ta Boko Haram da ke gwagwarmaya da makamai a wadannan jihohi.

Tuni dai majiyoyin a fadar shugaban kasar suka ce mahukuntan kasar na duba yiwuwar tura kantomomin soja da nufin jan ragamar jihohin wanda da dama ke ganin hakan ka iya iya jawo tada jijiyar wuya tsakanin gwamnati da 'yan adawa wanda ke yi wa tsarin kallo na daban duba da yadda kakar zabe ta 2015 ke dab da kamawa.

Ko a cikin makon jiya dai alal misali babbar jam'iyyar adawar kasar ta APC ta nemi da a kaddamar da bincike na kasa da kasa da nufin rarrabe tsaki da tsaba dangane da rikicin da ya gagari soja amma kuma mafarauta ke neman cin karfinsa a halin yanzu kamar yadda aka gani a wasu garuruwa na jihar Adamawa.

Nigeria Goodluck Jonathan
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce gwamnatinsa na kokarin kawo zaman lafiyaHoto: AFP/Getty Images

Wani kalubale da wannan bukata ta fadar shugaban kasa har wa yau ka iya fuskanta shi ne samun sahalewar 'yan majalisar dattawan kasar don tuni Sanata Abdulkadir Alkali Jajere ya ce shi da takwarorinsa na bangaren adawa za su sa kafa su shure wannan bukata domin a cewarsa basu ga abinda wa'adin baya na dokar ya tabuka ba wajen wanzar da zaman lafiya a jihohin.

Symbolbild Nigeria Armee
'Yan Najeriya sun ce sojin kasar sun gaza wajen kawar da aiyyukan ta'addanciHoto: picture alliance/AP Photo/Gambrell

Haka ma dai abin yake a majalisar wakilai inda nan ma ake hasashen ganin takaddama mai zafi a zauren wanda yanzu haka muradu na siysar 2015 ke jan akalar lamuransu maimakon mutunta bukatar fadar gwamnatin kasar ta Aso Rock.