1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon gwamnan Ogun ya mika makamansa

Uwais Abubakar Idris LMJ
June 26, 2019

A Njeriya batun mika mukamai har da motocin sulke da tsohon gwamnan jihar Ogun Ibikunle Amosun ya yi ga jami'an 'yan sanda, ya janyo mai da martani kan illar da hakan ke da shi ga yanayin tsaro da siyasar kasar.

https://p.dw.com/p/3L8tw
Schweiz Abstimmung EU-Waffengesetz
Hoto: Reuters/D. Balibouse

Wadannan makamai da ake cece-kuce a kansu dai, an bankado cewa gwamnan na Ogun ya mika bindigogi kirar AK47 da alburusai har guda milyan hudu da motocin sulke na yaki kirar APC. A kwanakin karshe na kammala wa'adin mulkinsa ya taso da batutuwa na matsalar yawaitar watsuwar makamai a Najeriyar. Tuni dai kungiyoyin rajin kare dimukuradiyya da hakkin dan Adam da suka fara nuna damuwa a kan lamarin musamman da yadda aka dauke shi a yanzu, musmman bisa la'akari da fuskantar rigingimu na amfani da makamai a lokutan zabe.

Koda yake bayan bullar wannan bayani Sanata Amosun ya yi kokari na kare kansa cewa ya dai mikawa kwamishinan 'yan sandan motocin sulke na yaki da wasu makamai, amma babu batun bindigogi a ciki. A yayin da ake takaddama a kan wannan batu tsakanin tsohon gwamnan da kwamishinan 'yan sandan da ya karbi makaman, bayanai na nuna cewa gwamnatin Najeriya ta ce da iznin gwamnati ne tsohon gwamnan ya shigo da makaman.

DW ta yi kokarin jin ta bakin jami'in yada labarai na rundunar 'yan sandan Najeriyar hakan yaci tura. Abin jira a gani shi ne yadda za a kwashe da wannan batu, a daidai lokacin da kungiyoyin kare hakin dan Adam ke bukatar dole a bincika lamarin, domin a baya akwai gwamnonin da suka nemi izinin shigo da makaman kamar gwamnan Zamfara amma gwamnati ta hanasu.