1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon ministan harkokin wajen Jamus ya ce ba ya jin Iran zata karkata daga shirinta na nukiliya

August 5, 2006
https://p.dw.com/p/Bunj

Bayan wata ziyara da ya kaiwa birnin Teheran tsohon ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer ya ce fata kadan ya rage ko Iran zata dakatar da shirinta na nukiliya da ake takaddama akai. Fischer ya fadawa mujallar Der Spiegel ta nan Jamus cewa ko da yake baya tsammanin Iran zata yi fatali da bukatun kwamitin sulhu na MDD, amma ba ya jin zata ba da amsa mai gamsarwa. Fischer, wanda a tsakiyar wannan mako ya yi shawarwari a birnin Teheran, ya ce yanzu masu tsattsauran ra´ayi ke kara samun fada a ji a Iran. Kwamitin sulhun MDD ya bawa hukumomin Iran wa´adin nan da 31 ga watannan na agusta da su dakatar da aikace aikacen saraffa sinadarin uranium.