Tsohon Shugaba Issoufou ya juya wa Bazoum baya
September 26, 2023Gishiri ya kama kan kaza dangane da yunkurin tsohon shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou da ya bijiro da shirin kawo goyon baya ga sojojin da suka yi juyin mulki. Dama tun a baya, jama'a na nuna shakkunsa kan lamarin, ganin cewa wadanda suka yi juyin mulkin sun yi gadin fadar shugaban kasa na tsawon shekaru karkashin Issoufou da ma Bazoum. Amma wannan sabon kutse na tsohon shugaban kasa ya sanya wasuhadiman Bazoumna ganin cewar akwai lauje cikin nadi, ciki har da Sahanine Mahamadou wani na PNDS-Tarayya ta yi martani ga firaministan da hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum.
Karin bayanPNDS Tarayya ta yi martani ga firaministai:
Sai dai na hannun daman tsohon shugaban kasa Mahamadou Issoufou suka ce ba shi ne ya yi wannan kira ba, amma jam'iyyar PNDS-Tarayya ce ta yi kiran. Amma Zakari Oumarou tsohon gwamnan jihar Maradi kuma mashawarci a fadar shugaban kasar da aka hambarar ya ki cewa uffan domin ba shi ne shugaban kwamitin ba. A nasu bangaren, 'yan kungiyoyin farar hula da ke fafutikar neman 'yancin kasar Nijar ta hanyar samun sabuwar akibla da sabon yanayi na tafiyar da mulki na ganin wannan lamari na jam'iyyar PNDS-Tarayya a matsayin batu da ba za a yarda da shi ba, a cewar Dambaji Son Allah.
Karin bayanNijar da Faransa an raba gari kwata-kwatai:
Wannan cece-kuce na zuwa ne daidai lokacin da kasar Faransa ta janye sojojinta daga Nijar da kuma jakadanta, lamarin da ya sa hukumomin na Nijar maida martani ta bakin Kanal Amadou Abdourahamane da ke magana da yawun sojojin na hukumar CNSP. A hannun daya kuma baraka na ci gaba da tabbata a jam'iyyar PNDS-Tarayya da ta mukii kasar ta Nijar sama da shekaru 12 da suka wuce, inda yanzu ta tabbata cewa ba a ga maciji tsakanin hambarren shugaban kasar Mohamed Bazoum da tsohon shugaban kasa Mahamadou Issoufou.