1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaItaliya

Von der Leyen za ta ziyarci Italiya

September 17, 2023

Kasar Italiya ta kadu da kwararar bakin haure da ba ta taba gani ba a shekarun baya-bayan nan bayan isar wasu kwakwale shake da dubban mutane a tsibirin Lampedusa.

https://p.dw.com/p/4WQ9h
Italiya I Bakin haure I LampedusaHoto: Cecilia Fabiano/AP Photo/picture alliance

Shugabar hukumar gudanarwar Tarayyar Turai Ursula Von der Leyen na shirin kai ziyara  Tsibirin Lampedusa, tare da rakkiyar Firaministar Italiya Giorgia Meloni don gane wa idanunsu dabban bakin hauren da aka sanar da isowarsu tsibirin. Firaminstar Italiya ta bukaci dauki daga EU bayan da a tsukin kwanakin uku aka sumu kwakwarowar bakin haure sama da 8.500 a tsibirin da ke a nisan kilomita 145 da kabar ruwan Tunisiya. Hotunan bidiyon dubban bakin hauren da aka nuna suna kwance a filin Allah, wasu kuma na tsallaka shingayen tsibirin domin fantsama cikin gari ya fusata wasu mambobin gwamnati Italiya, lamarin da mataimakin Firaministar kasar Matteo Salvini ya alakanta da barazanar mamayasu.