1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya: Imamoglu ya lashe zaben Magajin Garin Santanbul

April 1, 2024

A Turkiyya, Ekrem Imamoglu na babban jam'iyyar adawa ta CHP ya bayyana nasarar lashe zaben magajin garin Santanbul.

https://p.dw.com/p/4eIxq
Ekrem Imamoglu na babban jam'iyyar adawa ta CHP ya lashe zaben magajin gari a Santanbul
Ekrem Imamoglu na babban jam'iyyar adawa ta CHP ya lashe zaben magajin gari a SantanbulHoto: OZAN KOSE/AFP

Ekrem Imamoglu na babban jam'iyyar adawa ta CHP ya lallasa dan takarar jam'iyya mai mulki ta Shugaba Erdogan. Imamoglu mai shekaru 52 da haihuwa ne dai ya fara zama magajin garin Santanbul a shekarar 2019.

Karin bayani: Zaben Turkiyya:Yan adawa ne a kan gaba a Istanbul da Ankara

Ana dai ganin nasarar ta Imamoglu ya kara tabbatar da matsayinsa na madugu adawar Turkiyya a wani sabon salo ga shugaban kasar Recep Tayyip Erdogan da jam'iyyarsa da suke kokarin sake kwato manyan biranen kasar.

Zaben na ranar Lahadi dai an gudanar da shi ne a daidai lokacin da kasar ke fuskantar matsalar tsadar rayuwa da kuma faduwar darajar kudin kasar na Lira.