Turkiyya na bincike kan musabbabin gobarar gidan gala
April 2, 2024Kimanin mutane 29 ne suka mutu sakamakon gobarar gidan galan a birnin Istanbul yayinda wasu da dama suka jikkata. Jami'an hukumar kashe gobara sun bayyana cewa gobarar ta tashi da misalin karfe 12:47 na dare agogon Turkiyya wato 9:47 agogon UTC, a wani rukunin gidajen da ke yankin Turai na kasar.
Karin bayani: An kai hari wata mujami'a a Turkiyya
An rufe gidan galan gabanin azumin watan Ramadan domin gudanar da wasu gyare-gyare kafin daga bisani gobara ta tashi a wajen, kamar yadda jaridar Hurriyet ta rawaito.
Karin bayani: Turkiyya: Imamoglu ya lashe zaben Magajin Garin Santanbul
Magajin garin birnin da aka sake zabarsa a kwana-kwanannan Ekrem Imamoglu ya isa wajen da lamarun ya faru, tare da fatan cewa ba a samu karin wadanda suka rasa rayukansu ba.