1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine: Karbe iko da garuruwa ko kufai?

Ramatu Garba Baba LMJ
September 14, 2022

Sama da watanni shida da fara gwabza fada a tsakanin Rasha da Ukraine, fadar Kremlin ta yi nasarar kwace wasu muhinman wurare a Ukraine baya ga mamaye cibiyar nukiliyar Zaporozhzhia.

https://p.dw.com/p/4Gq1B
Rasha| Ukraine | Kharkiv | Yaki
Sojojin Ukraine a yankin Kharkiv na kasar da suka sake karbe iko da shi daga RashaHoto: Kostiantyn Liberov/AP Photo/picture alliance

Yankuna masu yawa ne dai Rashaan ta kwace tun bayan barkewar yakin, ciki har da tashar nukilya mafi girma a nahiyar Turai ta Zaporozhzhia da ke sanya fargaba a zukatan duniya. Mahukuntan na Kyiv din, sun ce sun sami gagarumar nasara a martanin da suka mayar kan rundunar sojojin Rasha a yankin Kharkiv. Kasashe masu goyon bayan Ukraine sun yaba da wadannan nasarorin, inda Shugaba Joe Biden na Amirka ya jinjinawa rundunar sojojin Ukraine din. Kasar Ostiraliya ma ta yabi shugaba Volodymr Zelensky na Ukraine, kan hazakarsa da jajircewar da shi da 'yan kasarsa suka nuna a yaki da Rasha.

Firaministan Ostiraliya Anthony Albanese ya ce hakan abin alfahari ne, sai dai kuma ya yi kira ga makusantan Shugaba Vladimir Putin kan su ba shi shawarar kawo karshen yakin. A halin da ake ciki ma dai, wuraren da rundunar Rasha ta lalata tashar samar da hasken wutar lantarki, gwamnatin Ukraine ta soma yin gyara sakamakon wadannan nasarorin da ta ayyana samu. Sai dai kuma abin da ke ci gaba da daure kawunan gwamnatoci, shi ne yadda aka gagara sanin mataki na gaba da Shugaba Putin zai dauka bayan shafe watannin shida da soma gwabza wannan yakin.