1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Najeriya ta nuna fushi kan rikicin Ukraine

February 28, 2022

Wannan kira na zuwa ne a daidai lokacin da zargin nuna wariyar launin fata ga 'yan Afirka mazauna Ukraine da ke son guje wa yakin da ake yi a kasar ke kara kamari. 

https://p.dw.com/p/47j7G
Muhammadu Buhari, Präsident von Nigeria
Hoto: Siphiwe Sibeko/REUTERS

Najeriya ta yi kira ga jami'an kan iyaka a Ukraine da sauran kasashe makwabta da su mutunta 'yan kasarta da ke Ukraine. Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan yada labarai Garba Shehu ya ce Najeriya ta samu rahotanni marasa dadin ji na yadda ake hana 'yan kasarta hawa motocin safa-safa da jiragen kasa domin shiga kasar Poland da sauran kasashe. Ya kuma ce akwai rahoton da ke nuna cewa kasar Poland ita ma ta fara hana 'yan Najeriya da ke Ukraine shiga kasarta.


Najeriyar ta ce yana da muhimmanci a mutunta kowa da kowa ba tare da nuna wata alfarma ba. Sai dai tuni ofishin jakadancin Poland da ke Najeriya ya musanta zargin, a yayin da ake dakon jin martanin ofishin jakadancin Ukraine a Najeriya kan wannan batu da ke ci gaba da daukar hankalin kasashen duniya.