1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Sojoji za su yi farautar 'yan IPOB

Muhammad Bello
July 13, 2023

Rundunar sojin Najeriya ta ba da umarni ga jami'anta da ke aikin tsaro a yankin Kudu maso Gabashin kasar, da su bazama don gano mabuyar 'yan rajin Biafra na IPOB.

https://p.dw.com/p/4TrKw
Nigeria pro-Donald-Trump-Kundgebung der Indigenous People of Biafra in Port Harcourt
'Yan IPOB masu rajin neman kafa kasar Biafra Hoto: Getty Images/AFP

Umarnin yin sintirin sojojin Najeriyar, na gano dukannin mabuya ta 'yan tada hankula a yankin na Kudu maso Gabashi, da a ke zargin 'yan rajin Biafra ne na IPOB ya fito ne daga bakin shugaban rundunar soji na Najeriya, Manjo janar Taoreed Lagbaja. Kuma umarnin ya ce dakarun sojin musamman a shiyyar 82 div da ke Enugu, su za su yi wannan aiki.

Aikin kuma da ke nufin sojojin su bi kurda kurda, walau cikin biranen jihohin yankin, ko kuma garuruwa ko kauyuka da ma dazuzzuka, da ake zargin 'yan IPOB din da ke karkashin jagorancin Nnamdi Kanu da tuni ya ke tsare hannun hukumomi a kasar na makalkale.

Rundunar ta soji dai ta ce ba za ta lamunci dukannin wani yanayi na hanawa jama'a walwala ba a yankin, a dalili na wani umurnin dan ta'adda tare da cewar, umarnin kuma da ba ya cikin dokar kasa.

UK Protest in Unterstützung für Nnamdi Kanu
Masu neman a saki Nnamdi KanuHoto: Vuk Valcic/ZUMAPRESS.com/picture alliance

Kan wannan sabon yanayi na tunkarar 'yan ta'adda na kungiyar ta IPOB mai rajin ballewa daga Najeriya don kafa sabuwar kasa mai suna Biafra. Benny Okafor, wani dattijo a yankin ya ce:

"Hakika hukumomi a Najeriya za su iya daukar wannan mataki, domin su ne doka ke hannayen su, matsawar dai dakarun sojin za su yi aiki cikin yanayi na martaba doka, ko wane mutum na son ya zauna lafiya a duk inda ya ke, kuma abin da 'yan yankin na Kudu maso Gabashi ke nema ke nan, sai dai dole a yi la'akarin cewar ba amfani da karfi ne zai yi maganin matsalar ba, don ba yaki a ke ba, domin matsalar ba wata ba ce illa ta Nnamdi Kanu jagoran kungiyar ta IPOB, tun da dai tsare Kanu ne to a sake shi a gani".

Tsohon sakataren hulda da jama'a na kungiyar kabilar Igbo ta Ohaneze Ndigbo kuwa Mr Achi Opaga ya yi tsokaci kamar haka:

"Ina ganin matakin ke nan da ya kamata a ce rundunar soji ta dauka tubtuni, domin mu da gani mu ke rundunar ta soji na jin dadin abin da ke faruwa a yankin ne, don da sojojin sun afkawa matsalar tuni, da yanzu sai tarihi".

Nigeria IPOB Mitglieder
'Yan IPOB a NajeriyaHoto: STEFAN HEUNIS/AFP/Getty Images

Tun dai a watan Agusta na shekarar 2021 ne, kungiyar ta rajin Biafra ta IPOB, ta fara bada umarni ga jama'ar yankin na Kudu maso Gabashin Najeriyar, na su fara zaman dirshan a gida a duk ranar da jagoran IPOB din, Nnamdi Kanu zai gurfana a kotu, kuma daga bisani kungiyar ta maida zaman dirshan din a gida ya koma duk ranar Litinin, sannan kuma kwatsam sai a satin jiya kungiyar ta sanar da zaman dirshan din a gida na kwanaki bakwai kai tsaye. Kuma yanzu ma kungiyar ta ce sati biyu za a yi.