1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Vladimir Putin na Rasha ya yaba kokarin Chaina kan Ukraine

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
May 15, 2024

Mr Putin ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da kafar yada labaran Chaina ta Xinhua, gabanin ziyarar aiki ta kwanaki biyu da zai fara a Chainan daga ranar Alhamis

https://p.dw.com/p/4frT1
Hoto: Sergei Guneyev/Pool/picture alliance

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya yi jinjina ga kokarin da Chaina ke yi bil'hakki, don kawo karshen yakin da take yi da Ukraine.

Karin bayani:Chaina ta jaddada kudirinta na hade Taiwan

Mr Putin ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da kafar yada labaran Chaina ta Xinhua, gabanin ziyarar aiki ta kwanaki biyu da zai fara a Chainan daga ranar Alhamis, inda zai gana da babban amininsa shugaba Xi Jinping na Chaina, kamar yadda ya fada a tattaunawar.

Karin bayani:Chaina za ta hada hannu da Rasha don magance rikicin Gaza

Ya kara da cewa baya ga batun yakin Ukraine, za kuma su tattauna da Xi Jinping kan sha'anin da ya shafi tattalin arziki, la'akari da irin takunkumin da Rashan ke fama da shi sakamakon mamayar Ukraine da ta yi sama da shekaru 2 da suka gabata.