An saki mutun 40 daga kurkuku a Masar
July 23, 2021Daya daga cikin wadanda aka sako ita ce wata fitacciyar ma'abociyar shafin sada zumunta na Facebook Esraa Abdel-Fatah. Mai shekaru 43 da haihuwa wace aka bada sunanta don samun lambar yabo ta Nobel, ta shafe kusan shekaru biyu a tsare bisar zargin yada labaran karya da kuma wasu tuhume tuhume na kin jinin gwamnati. Wani wanda shi ma ya sami 'yanci shi ne wani dan Jarida mai sukar lamirin gwamnati Gamal el Gamal wanda ya zauna a kasar Turkiyya shekaru yana gabatar da shirin Talabijin yana kuma sharhi a shafin Facebook. Jami'an tsaro sun damke shi jim kadan bayan da ya sauka a filin jirgin saman Alkahira a cikin wannan shekarar.
Karin Bayani : Shekara 10 da kaddamar da borin juyin juya hali a Masar
Ramy Yaacoub, darakan cibiyar dandalin Tahrir kan manufofin gabas ta tsakiya ya yi tsokaci game da sakin fursunonin yana mai cewa. "Yace na yi maraba har cikin zuciyata sakin baya bayan nan, saboda biyu daga cikin su mutane ne wadanda na san su fiye da shekaru goma. Farin ciki na ba zai misaltu ba, to amma na yi imanin cewa wannan ba ita ce masalaha ta karshe ba. Na yi murna mun samu an sako wadannan mutane, to amma akwai ire irensu da dama a tsare." Sakin baya bayan nan da aka yiwa yan fafutuka da yan jarida ya sha banban kwarai da irin dirar mikiyar da ake yi wa yan adawa yanzu haka a Masar. A wannan makon tsohon babban editan jaridar Al-Ahram da ake bugawa kullum Abdel Naser Salama, an tsare shi a bisa tuhumar ta'addanci da yada labaran karya. Haka ma a makon da ya gabata an cigaba da shari'a a babbar kotun shari'ar manyan laifuka ta Masar akan wasu yan fafutuka su shida da kuma yan jarida ciki har da wani tsohon dan majalisa Zyad el Elaimy.
Masar bata tausayawa kungiyoyin da kira 'yan ta'adda
Masar bata nuna tausayawa ko kadan akan yan kungiyar Muslim Brothers wadda aka ayyana ta a matsayin kungiyar ta'adda a shekarar 2013. A watan Yuni aka yanke hukuncin kisa akan yan kungiyar su 12 a Masar. A yanzu iyalansu sun kaddamar da wani kamfe da suka yi wa lakabi da maudu'in #StopEgyExecutions domin adawa da aiwatar da kisan. Daya daga cikin wadanda aka yankewa hukuncin kisan shi ne Mohammed El-Beltagy wani fitacce a gwagwarmayar juyin juya halin Masar a 2011.
Matarsa Sana Abd al-Gawad ta rubuta wasikar koke inda ta zargi hukumomin Masar da tauye hakkin wadanda aka tsare. Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Rights Watch ta yi kiyasin cewa akwai mutane kimanin 60,000 wadanda a yanzu haka ake tsare da su a Masar bisa dalilai na siyasa. Kasar ita ce kan gaba a jadawalin Amnesty International na kasashen da suka aiwatar da hukuncin kisa a 2020 adadin da rubanya har sau uku daga mutum 32 a 2019 zuwa 107 a 2020.
Karin Bayani: Takaddama kan Kogin Nilu taki karewa
Masar na fuskantar matsin lamba na aiwatar da sauye sauye inda Amirka ta yi kakkausar suka kan tsare yan adawa. Mohammed El Dahshan masanin al amuran gabas ta tsakiya da arewacin Afirka a cibiyar nazarin siyasar duniya Chatham House da ke birnin London ya yi bayani da cewa. "Yace hakika matsin lambar kasashen duniya na iya sa shugaba al Sissi da gwamnatin Masar su sauya halayyarsu. To amma maganar gaskiya ita ce bamu ga wani ya yi wannan yunkurin da gaske ba. Misalin da za mu iya nuni da shi na baya shi ne bayan da shugaba al Sissi ya hau karagar mulki a 2013 kuma musamman kisan da aka yiwa masu zanga zanga tsakanin 800 zuwa 1000 a rana guda a watan Augusta. Amirka ta ce za ta jinkirta bai wa Masar makaman soji, a saboda haka suka daina bada tallafi ta fuskar makaman soji. Amma maganar ita ce a duk lokacin da wani ya yi alkawarin amfani da karfin tasiri akan gwamnatin Masar dangane da ketta haddin bil Adama basa aiwatarwa bil hakki da gaskiya." Abin jira a gani dai shi ne Masar za ta sauya taku kan hakkin bil Adama domin kyautata kimar ta a idanun duniya ko kuwa sakin fursunonin wani abu ne kebabbe da akan yi a dukkan hutun shekara.