1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekara 10 da borin juyin juya hali a Masar

January 12, 2021

A watan Janairun shekara ta 2011 kimanin mutane 25,000 sun yi zanga-zangar neman tabbatar da tsarin dimukuradiyya a birnin Alkahira na kasar Masar domin neman kawo karshen gwamnatin Shugaba Hosni Mubarak.

https://p.dw.com/p/3nokC
Ägypten Tahrir-Platz Proteste 2011
Hoto: picture-alliance/dpa/F. Trueba

Shekaru 10 ke nan da zanga-zangar mai tasiri a Masar, wadda a makonni da watannin da suka biyo bayanta, ta kai wasu kasashe makwabta da ake kira juyin-juya halin kasashen Larabawa, wanda ya kasaita daga bisani.

Wannan zanga-zangar ta galibi matasa da manoma gami da masana da suka hada da mutane kamar Alaa al-Aswani marubuci. Kuma shekaru 10 bayan wannan gagarumar zanga-zanga Alaa al-Aswani ya samu kansa cikin zaman gudun hijira a birnin New York na kasar Amirka, wanda ya nuna takaicin yadda kasar Masar ta sake komawa karkashin mulkin kama-karya.

Karin bayani: Shekaru biyar da juyin juya hali a Masar

"Na yi imanin mutanen Masar yanzu, duk da suna rayuwa karkashin mulkin mallaka, 'yan Masar da ke rayuwa ba su ba ne gabanin juyin-juya hali. Kar a manta kashi 65 cikin 100 na 'yan Masar suna kasa da shekara 40 da haihuwa. Galibin matasa da suka kawo sauyi, za su ga bayan yanayin da ake ciki, ina da karfin gwiwa kan haka."

Alaa al-Aswani, murubuci dan kasar Masar da ya tsere zuwa Amirka
Alaa al-Aswani, murubuci dan kasar Masar da ya tsere zuwa AmirkaHoto: picture-alliance/Photoshot

Mafarkin Jamhuriya da aka wallafa a shekara ta 2018, littafi ne da ke magana kan zanga-zangar shekara ta 2011 kan sauyin cikin kwanciyar hankali da matasa suka jagoranta a Masar, gami da mafarkin samun sabuwar dama. Amma kuma akwai batun fada da masu zanga-zanga daga bangaren masu karfin fada a ji.

Akwai fata lokacin da Shugaba Hosni Mubarak ya yi murabus karkashin matsin lamba na masu zanga-zanga, amma 'yan mazan jiya sun ci gaba da kankane lamuran madafun iko. Marubuci Alaa al-Aswani yana cikin mutanen da suka fara zanga-zangar. Tsohon Shugaba Mubarak ya fuskanci tuhuma da dauri kan cin hanci da amfani da mukami ta hanyar da ta saba doka.

A shekara ta 2012, Mohammed Morsi na kungiyar 'yan uwa Musulmai ya lashe zaben shugaban kasa. Sai dai a shekara ta 2013 sojoji sun kifar da gwamnatin Morsi sannan aka kama shi, tun lokacin Abdel Fattah al-Sisi yake rike da madafun ikon kasar ta Masar kuma lamura sun kara sukurkucewa kan kama-karya. Marubuci Alaa al-Aswani ya yi karin haske.

"Ba mu da sauran 'yancin fadin albarkacin baki. An sani, kafofin yada labarai suna rubuta abin da aka amince kadai. Ina da sauran abokai kalilan a Masar, masana, wadanda ba sa fursuna. Galibin abokaina suna fursuna."

Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi
Shugaban Masar Abdel Fattah al-SisiHoto: Costas Baltas/AP Photo/picture alliance

Karkashin gwamnatin Abdel Fattah Al-Sisi an haramta rubutun Alaa al-Aswani, duk da yana cikin muhimman marubuta na kasar. Rubutunsa an wallafa cikin harsuna 60 kuma an sayar da miliyoyin kofi. Sabon littafinsa ba za a iya samu a kasar Masar ba. Alaa al-Aswani yana sane da cewa duk da yanayin, littafinsa na ci gaba da samun karbuwa saboda ayyukan bayan fage.

"Ina da makwabciyar kirki, mata mai kirki, wadda ta kira littafin wani juyin-juya hali. Ta ce ta karanta littafin kuma abokaina suna gaya mun abin da suka fahimta. Amma ban sauya ra'ayina kan abin da na rubuta ba. Kuma bayan makwabciyata ta karanta littafin, ta kira ni a nan New York ta ce ta ji dadin littafin. Kuma tahirin duniya ya dangana kan abin da aka rubuta."

Al-Aswani ba da son ransa ya tsere daga Masar ba. Amma lokacin da kotun musamman ta soja ta yi barazanar tuhumarsa kan cin zarafi a shekara ta 2017 ya tsere zuwa birnin New York na kasar Amirka.