Wane ne Attahiru Jega?
March 26, 2015A yayin da ake shirin gudanar da zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki a Tarayyar Najeriya, za a iya cewa shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar INEC Attahiru Muhammadu Jega na cikin tsaka mai wuya. Tun dai a watan Fabarairun da ya gabata ne ya kamata a gudanar da zabukan, sai dai wasu dalilai na rashin tabbacin tsaro da hukumar tsaron kasar ta bayar, ya tilasta dage zabukan zuwa karshen wannan wata na Maris.
Tun a shekara ta 2007 ne dai shugaban Tarayyar ta Najeriya Goodluck Jonathan ya nada Farfesa Attahiru Muhammadu Jega a matsayin shugaban hukumar zabe mai zaman kanata ta kasar wato INEC, inda ya karbi jagoranci daga tsohon shugaban hukumar zaben Maurice Iwu. Tun bayan zabukan na 2007 dai an yi ta samun cece-kuce tare da bukatar samun shugaban da zai iya tafiyar da hukumar ta INEC yadda ya kamata. Sai dai a shekara ta 2011 ma an zargi hukumar ta INEC da yin kura-kurai masu tarin yawa musamman daga bangaren jam'iyyun adawa. A cewar Kole Shettima na cibiyar Dimokaradiyya da harkokin Raya kasa a Najeriyar, nadin na Jega abu ne da ya dace duba da irin halayyarsa.
"Ya kasance mai gaskiya da rikon amana, shi da kansa ya amince ya yi kuskure a zabukan 2011, misali yayin da ya ke bayani a gaban majalisar dattawa, ya bayyana cewa akwai katunan zabe masu tarin yawa da basu kai ga shigowa kasar ba. A sabo da haka ba ya son ya fadi karya ya na ji yana gani, wannan baya daga cikin dabi'unsa."
Shin ko wanene attahiru Jega?
Mai shekaru 58 a duniya ya kasance Farfesa a fannin kimiyyar siyasa, ya zauna a kasashen Birtaniya da Sweden kafin daga bisani ya koma jami'ar Bayero da ke Kano a Tarayyar ta Najeriya a matsayin mataimakin shugaban jami'ar. Ya kasance daya daga cikin mambobin kwamitin da aka nada domin kawo gyara a harkokin zabe a kasar bayan zabukan shekara ta 2007.
Bayan kammala zabukan shekara ta 2011 Jega ya bayyana shugaba Jonathan a matsayin wanda ya lashe zaben a karkashin jam'iyyar PDP mai mulki inda ya samu yabo daga 'yan wannan jam'iyya. Sai dai a cewar wani mai fashin baki kan al'amuran siyasa a jihar Kano Mohammad Junaidu, jam'iyyar PDP ta yi amfani da katunan zabe na wucin gadi a wancan lokaci wajen yin magudi zabe, kana a wannan karo Jega ya daura damarar gudanar da zabukan da katunan zabe na din-din-din, wanda a ganin Junaidu shine ya fara jawo masa baraka da gwamnati mai ci yanzu ta yadda rahotanni suka nunar da cewa an sha yi masa barazana kan ya ajiye aikinsa:
"Ya san an ji kunya a shekara ta 2011 kunma shin da kansa ya fadi hakan, a ganina Jega na son ya dawo da kimarsa a idanun 'yan Najeriya tare da tabbatar da cewa a yanzu an yi zabuka cikin gaskiya da adalci da kuma inganci. Wannan shine tushen rigimarsa da gwamnati."
A nasa bangaren Jega ya sha alwashin gudanar da zabuka ba tare da nuna ban-banci ba, yana mai cewa....
"Bari in sake tabbatar muku da cewa INEC da dukkan ma'aikatanta za su gudanar da zabuka ba tare da nuna ban-bancin siyasa ko bangaranci ba a yayin zaben. Muna aiki tare da jami'an tsaro domin tabbatar da cewa an gudanar da zabukan lami lafiya."
Jega ya kara da cewa za su fitar da sakamakon zabukan tare da bugawa a shafin Internet na hukumar ta INEC domin kowa ya gani ya kuma tabbatar da sahihanci da ingancin zaben.