Sheikh Dahiru Bauchi da gudunmawarsa
July 10, 2024An haife Sheikh Dahiru Usman Bauchi ne a ranar biyu ga watan Muharram na shekara ta 1346 bayan hijirar fiyeyyen halitta annabi Muhammad SAAW, abin da ya sa a lissafin shekarar hijiriyya ta Musulumci ya cika shekaru 100 a duniya. Koda yake a lissafin shekarar miladiyya an haife shi ne a shekara ta 1927, ke nan sai a shekara ta 2027 ne zai cika shekaru 100. Cikin tattaunawarsa ta musamman da tashar DW Hausa, Sheikh din ya yi jinjina da addu'o'i ga tashar da kuma yin nasiha ga sauran al'ummar Musulmin duniya baki daya. Tarihi ya nunar da cewa Shehin na da shekaru 10 a duniya ya haddace al-Qur'ani mai girma, sannan yana da shekaru 20 a duniya ya fara karantarwa da hidima ta da'awa yanzu kimanin shekaru 80 kenan yana gwagwarmaya da hidima ga addinin Musulumci kana yana da 'ya'ya mahaddata a kalla 73 da kuma jikoki sama da 200.