Warware takaddama kan ranaikun zabe a Najeriya
March 2, 2018Ja in ja da ake yi a game da wane ne ke da iko na sanya ranaikun da ma tsarin da za a gudanar da zaben a Najeriya na ci gaba da zama babban al'amari a kasar, abin da ya sanya kallon fitar da ranaikun da za a gudanar da zabubbukan tun daga 2019 har zuwa 2055 a matsayin muhimmin mataki da hukumar zaben ta INEC ta dauka.
Domin hukumar ta bayyana cewa bisa tsari na demokuradiyya a kasashe da dama al'umma ta san ranaikun da za a gudanar da zabe domin kaucewa cece-kuce da ma shaci fadi.
Mallam Aliyu Bello mataimakin darakta ne a hukumar zaben ta Najeriya ya bayyana abin da hukumar ke nufi da wannan tsari.
"Bisa hasken dokar da take kasa yanzu ta kundin zabe na 2010 kamar yadda aka yi masa gyara, wanda hukunmar zabe ta yanzu ta dora cewa ana yin zabe a ranar Asabar ta biyu ta watan Fabrairun shekarar zabe, to za ka iya gano ranar zabe na shekaru masu yawa nan gaba. Wannan tsari da aka saba a kasashe masu ci gaban demokuradiyya da ba a san shi ba a Najeriya, amma yanzu ake son a dora ta kan matashiyar sanin ranaikun zabe."
Ko mene ne muhimmancin wannan mataki a yanzu da hukumar zabe ke son Najeriya ta bi sahu da tsari na kasashen duniya a kan ranaikun zabe?
Barrister Mainasara Umar mai sharhi ne a kan dokokin demokurdiyya a Najeriya.
"Hakan na nufin demokuradiyya ta samu gindin zama ke nan a Najeriya. Tun da akwai tanade-tanade na shekaru 36 masu zuwa. Wannan abu ne na alheri da zai sa kowa ya shirya."
A yayin da ake ci gaba da takaddama a kan sauya ranaikun zaben da majalisun dokokin Najeriyar suka yi, kwararru a fannin demokuradiyyar Najeriya na bayyana takatsantsan a kan lamarin.
Abin jira a ganin shi ne abin da zai biyo baya a wannan lamari da ke daukar hankali a daidai lokacin da aka kada kugen siyasar Najeriyar.