Labarin Wasanni: United ta sha kashi
March 6, 2023Wannan cin dai, ya dauki hankalin masu sha'awar wasan kwallon kafa a duniya baki daya. Sannan Chelsea ta doke Leeds da ci daya mai ban haushi, kana Arsenal ta lallasa Bournemouth da ci uku da biyu yayin da a daya bangaren Manchester City ta samu galaba a kan Newcastle da ci biyu da nema. A yanzu haka dai kungiyar Arsenal ce ke jagoranci da maki 63, a matsayi na biyu akwai Manchester City mai maki 58 kana Manchester United tana matsayi na uku da maki 49.
A wasannin La Liga ksar Spaniya kuwa, Betis da Real Madrid sun tashi babu ci yayin da Barcelona ta doke Valencia da ci daya mai ban haushi, inda ita kuwa Atletiko Madrid ta lallasa Sevilla da ci shida da daya kana Valladolid ta doke Espanyol da ci biyu da daya. Kungiyar Barcelona ke jagorancin teburin na La Liga da maki 62, yayin da a matsayi na biyu akwai kungiyar Real Madrid mai maki 53, kana Atletiko Madrid tana matsayi na uku da maki 45.
Faransa kuwa an kafa tarihi, inda Kylian Mbappe na kungiyar Paris St Germain ya zama dan wasan da ya fi zura kwallo a raga ga kungiyar. Mbappe dai yana cikin 'yan wasan Faransa da tauraruwarsa ke haskawa a duniyar kwallon kafa yanzu haka. Shi dai Kylian Mbappe bai jima da tsawaita kwantiraginsa da kungiyar ta Paris St Germain ba.
A wasannin lig na Jamus kuwa, Bayern Munich ta bi Stuttgart har gida ta doke ta da ci biyu da daya kana Leverkusen ta samu galaba a kan Hertha Berlin da ci hudu da daya. Augsburg ta samu nasara a kan Werder Bremen da ci biyu da daya, sannan Wolfsburg ta tashi biyu da biyu a fafatawar da suka yi da kungiyar Eintracht Frankfurt.
Masana harkokin wasan kwallon kafa a Najeriya kuwa sun bayyana gamsuwa dangane da irin ci-gaba da ake samu a fagen gasar kwallon kafa ta Premier a kasar sakamakon sababbin sauye-sauye da ke wakana a tsakanin hukumomin da ke kula da wasannin.