Dortmund ta doke Bayern da ci 2-0
August 5, 2019A karshen mako an gudanar da wasan da ake yi wa lakabi da Supercup na fita da gwani na gawanaye wanda ya hada Bayern Munich da ke rike kambun zakara da kuma Borussia Dortmund. Wannan wasa ne bisa ga al'ada ke yaye kallabin kakar gasar Bundesliga, kuma Borussia Dortmund ta samu nasara da ci 2-0 a kan Bayern Munich, duk da cewa sabbin 'yan wasa uku da ta sayo ba su yi wasa ba ciki har da Thorgan Hazard, Julian Brandt da Mats Hummels. Su 'yan wasan na Dortmund sun fi nuna hazaka bayan da aka dawo hutun rabin lokaci, inda a minti 48 da fara wasa Paco Alcacer ya zura kwallon farko, yayin da Jadon ya zira ta biyu a minti 21 kafin a yi busan karshe.
A wasu kasashen Turai da kwallon kafa ke da tagomashi ma dai, an gudanar da irin wannan wasa na fidda gwani na gwanaye, inda a Ingila ake kiransa Community Shield wanda aka yi tsakanin Manchester City da Liverpool, inda 'yan wasan Manchester City suka ci nasara a bugun daga kai sai mai tsaron gida da ci biyar da hudu. Wannan dai shi ne kofi na hudu da City ta lashe a wannan shekarar.
A nahiyar Afirka, a wannan karshen mako, kungiyoyin kasashe dabam-dabam sun ci gaba da kalubalantar junansu da nufin samun damar shiga gasar kwallon kafa ta 'yan wasa da ke bugawa a cikin gida da za ta gudana a 2020. Bayan tankade da rairaye kungiyoyin da suka cancanci zuwa zagaye na gaba sun hada da eSwatini, Mauritania, Uganda, Senegal, Zambia, Burundi, Ethiopia, Equatorial Guinea, Lesotho, Madagascar, Mali, Namibia, daga Tanzaniya, Togo da Zimbabwe.
Za a ci gaba da wasannin share fagen har i zuwa watan Oktoba. Kasashe 15 ya kamata su samu tikitin hayewa baya ga kasar Kamaru da za ta karbi bakoncin gasar.
A Najeriya, duk da nasarar da kasar ta samu a karon farko bayan shekaru da dama a fannin tseren keke inda ta lashe gasar kasashen Afirka da aka yi a Abuja, amma tana ci gaba da kasance a baya sosai a wannan fannin na tseren idan aka kwatanta da sauran wasanni na kasa da kasa da Najeriya ke shiga kamar kwallon kafa.