February 10, 2020
Talla
Babbar kungiyar kwallon kwando ta mata ta Najeriya D Tigress ta samu tikitin shiga wasannin Olympics na 2020 a Tokyo, duk da cewa ta sha duka 64-70 a hannun Sabiya a ranar Asabar, a wasan rukuni na biyu a gasar wasannin neman cancanta. Tawagar Najeriya ta samu wannan dama ce bayan kokarin Mozambik na cancanta ya ci tura sakamakon mummunan duka ci 49-124 a hannun Amerika da ke rike da kofin duniya na basket-ball.
A ranar Lahadi ma 'yan matan na Najeriya sun kara da takwarorinsu na Amerika wasan rukuninsu na uku, wanda hakan ba zai yi tasiri ba a wasannin neman shiga wasannin Olympics na 2020.
Hukumar kwallon Kwando ta Najeriya NBBF ta kafa tarihi wajen kasancewa kungiya daya tilo da za ta samu wakilai biyu a Gasar Olympics.