Wayoyin "Smart phones" na kamfanin Google ga Afirka
September 30, 2015Yanzu dai a iya cewa kamfanin na Google ya yi nisa wajan samar da wayoyin komai da ruwanka da ake kira Smartphone a turance a kusan kafatanin kasashen nahiyar Afirka. Ana kuma iya samun manya daga cikin ire-iren wadannan wayoyi cikin farashin da za a iya kiransa mai rahusa, domin kuwa a kan same su a kasa da dalar Amurka 80, wato kwatankwacin kasa da Naira 20,000 kamar yadda Gladys Nwachukwu da ke zama kwararriya a fannin wayoyi irin na zamani ta bayyana.
"Wayoyi ne masu kyau, kana kuma da karko, ga araha wadanda kuma masu karamin karfi za su iya mallakarsu, gaskiya a nawa ra'ayin suna da kyau."
Shi dai kamfanin na Google ya samu karbuwa sosai a nahiyar Asiya ta hanyar samar da wayoyi masu kyau da kuma araha, haka kuma yana dauke da ingantattun fasahohin zamani da suka hada da shafukan bincike, ga kuma yanar gizo, kana da shafukan hotunan bidiyo.
Wayoyi masu amfani daban-daban
Har ila yau wayoyin ba su tsaya ga nan ba domin kuwa suna dauke da Sim guda biyu, baturansu kuma ga karko, sannan kuma a kan iya kama tasoshin FM da dai sauransu. Rushabh Doshi masani ne a fannin nazarin fasaha ya yi karin haske kan wayoyin na Smartphones.
"Su dai wayoyin komai da ruwanka an kirkiresu ne don amfani da yawa ga al'umma. Don haka nake bada tabbaci ga jama'ar da suke ta'ammali da su cewar kada su ji shakku wajan cigaba da amfani da su a matsayin abokan rayuwa ta yau da kullum. Haka abin yake ga masu kasuwanci domin kuwa wayoyin ba su tsaya a nan ba. Har ila yau sukan zama abokan huldar kasuwanci ta hanyar karin samun kudaden shiga ga harkokin kasuwancin bil Adama."
Barazana ga kamfanonin Afirka
Yanzu dai irin wadannan wayoyin sun zama ruwan dare gama duniya a nahiyar Afirka da ake kiransu Hot 2, musammam ma kasashe irinsu Najeriya da Kenya da kuma Cote d'Ivoire, kamar yadda Gladys Nwachukwu ta yi tanbihi a kai.
"Sababbin da za su zo a nan gaba kadan, za su zo da sabbin manhajoji wadanda aka sake zamanantar da su. A takaice dai suna da 'yar tsada, idan aka kwatantasu da na da, sai dai kuma an dada kyautatasu kamar yadda masu iya magana kan ce iya kudinka iya shagalinka."
Sai dai kuma dangane da yadda kayayyakin da kamfanin na Google ke samarwa ke samun karbuwa a kasuwannin Afirka, hakan ka iya zama barazana ga sauran kamfanonin da suke da aniyar tallata tasu hajjar a kasashen na Afirka.