WHO: Cutar Polio ta sake bayyana a Najeriya
August 12, 2016Yara biyu ne a jihar Borno Arewa maso gabashin kasar kawowa yanzu suka sami nakasa ta sanadin cutar a cewar hukumar mai cibiya a birnin Geneva. Ta ce a jihar ta Borno yankuna irin na Gwoza da Jere sun kasance na da wahalar shiga a aikin rigakafin cutar hakan ya sanya sake bayyanar cutar. Abin da a cewarta nakasu ne ga kokarin kasar ta Najeriya na kawar da cutar baki daya, musamman a burinta na ganin bayanta nan da shekarar 2017.
Michel Zaffaran darakta ne a Hukumar Lafiya ta Duniya WHO:
"A jiya mun bayyana samun bullar cutar ta Polio a Arewacin Najeriya, wannan dai ba karamin koma baya ba ne a kokarinmu na kakkabe cutar kasancewar a ranar 24 ga watan Yuli Najeriya ta yi biki na shekaru biyu ba tare da sake bullar cutar ba."
Zaffaran ya ce kawowa ranar Alhamis kasashe biyu ne wannan cuta ke nan daram Pakistan da Afghanistan, yanzu da bayyanar wadannan yara biyu da cutar ta nakasa a kwai masu cutar 21 a duniya a cikin kasashen na Pakistan da Afghanistan da Najeriya.