1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

WHO: Kakkabe cutar Polio a Najeriya

Binta Aliyu Zurmi
August 25, 2020

Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO na shirin baiyana kawo kasrhen cutar shan Inna ko Polio a Afirka a wannan rana ta Talata.

https://p.dw.com/p/3hSY0
Nigeria Polio Virus Impfung
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Wolfe

Wannan mataki na zuwa ne bayan da hukumar ta ce an share sama da shekaru hudu ba tare da an sami cutar Polio a Najeriya ba, kasancewarta kasa ta karshe da ta yi ta fama da cutar. 

A sanarwar da shugaban Hukumar ta lafiya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya fitar, ya nuna godiya ga jami'an gwamnati da ma'aikatan lafiya da kuma masu bada gudumawa akan irin rawar da suka taka na kawo karshen cutar.