Mace ta farko a matsayin shugabar WTO?
October 28, 2020Tun da farko kakakin kungiyar ta WTO Keith Rockwell ya shaidawa manema labarai cewa, bayan da wakilai daga manyan rassan kungiyar uku na duniya suka kwashe watanni hudu suna tattaunawa da kasashe mambobinta, akwai yiwuwar su yanke shawarar zabar Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin shugaba.
Karin Bayani: WTO: 'Yan Afirka uku na neman shugabanci
Wakilai 26 cikin 27 ne dai suka bayyana amincerwasu da Okonjo-Iwela. Amirka ce kasa daya tilo da ta ki goyon bayan zabar Okonjo-Iweala a matsayin sabuwar shugabar kungiyar ba, inda ta goyi bayan ministar kasuwancin Koriya ta Kudu Yoo Myung-hee.
Karin Bayani: Taƙaddama kan kasafin kuɗin tarayyar Najeriya
Sai dai Za a tabbatar mata da kujerar ne, bayan kasashe mambobin kungiyar 164 sun yanke hukunci a babban taronta na ranar tara ga watan Nuwamba mai zuwa. Mai shekar 66 a duniya, Okonjo-Iweala ta kasance mace ta farko da ta zama ministar kudi da kuma ministar harkokin kasashen waje a kasarta Najeriya, kuma tana da kwarewar aiki ta tsawon shekaru.