1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zabukan gwamnoni daki-daki a Najeriya

Yusuf Bala Nayaya UB, MBB, NSZ, ASM, MAS, FM, AMK, YIJ, ZUD, MB
March 8, 2019

An dai yi zabukan gwamnoni 29 da na 'yan majalisa a jihohin Najeriyar. Sai dai akasari mutane ba su fita zabe ba kamar yadda aka zata. Ga yamutsi a wasu wuraren.

https://p.dw.com/p/3EgoQ
Nigeria Regionalwahlen
Hoto: Ma'awiyya Sadiq

Duk da cewar dai ana masa kallon na biyu a jeri na muhimmanci a tsakanin al’ummar tarrayar Najeriyar, zaben gwamnoni da na 'yan majalisu na jihohin da ke gudana na da tasirin gaske ga makoma ta dimukaradiyyar tarrayar Najeriyar a nan gaba.

An dai fafata a jihohi 29 da za su sake zabar gwamnoni, ko bayan majalisun dokoki na daukaci na jihohin kasar 36 da ke shirin sake zubi a cikin fatan karin karfi ga dimukaradiyyar kasar da ke dada girma.

Kano da Legas da Bauchi da Kaduna da Zamfara da Katsina da Taraba

Nigeria Präsidentschaftswahlen
Mutane da dama sun fita zabe a KanoHoto: picture-alliance/AP/S. Alamba

A jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya wakilinmu Nasir Salis Zango ya rawaito cewa an bude rumfunan zabe da wuri lamarin da ya sanya al'umma shiga ka'in da na'in lamuran zaben kuma mutane da dama sun fita zabe, haka nan a jihar Legas da ke yankin Kudu maso Yammacin Najeriya. A Kaduna Najeriya dai duk da cewa an yi zabe lafiya sai da al'umma suka rika kira cewa a fito kada kuri'a ta hanyar amfani da kafar sadarwar zamani da hanyoyin rediyo da amsa kowa saboda karancin masu fita zabe. A Zamfara kuwa isar kayan zabe da wuri duk da matsalar tsaro shi ya faranta rai na al'umma. A jihar Katsina mahaifar Shugaba Muhammadu Buhari, 'yan siyasa na APC da PDP na zargin junansu da amfani da kudi domin sayen kuri’u a zaben gwamna.

A wannan karo na zaben gwamna a jihar Bauchi wanda ake ganin jama’a za su fito fiye da yadda suka yi a zaben shugaban kasa, ya samu rashin armashi duk da ikirarin da mafi yawancin al’ummar jihar ke yi dangane da muhimmancin zaben a wajensu. A jihar Taraba ma dai an yi zaben lafiya duk da cewa sai da aka kai ga kama wasu jiga-jigai na siyasa da aka kama da aikata ba daidai ba.

Sokoto da Gombe da Nasarawa da Benue da Plateau da Rivers

Nigeria Akkreditierungs-Wähler
Ba masu zabe da yawa a GombeHoto: DW/Uwaisu A. Idris

Ko shakka babu al’umma sun yi fitar farin dango a sassa daban-daban na jihar Sakoto da muradin kada kuri’unsu to amma sai dai kuma da yawa daga cikin runfunonin zaben da wakilinmu Mu’awiya Abubakar Sadik ya zaga a cikin birnin na Sokoto duk da yake babu matsalolin na’urar tan-tancewa ko rashin malamman zabe kamar zaben da ya gabata, an samu tashin hatsaniya ta masu jefa kuri’u kamar a wata rumfa ta ‘Yar Goriba.

A jihar Gombe an samu karancin masu jefa kuri’a a yawancin mazabu idan aka kamanta da yadda mutane suka fita a zabukan shugaban kasa da ‘yan majasar dokokin tarayya da aka gudanar makonni biyu da su ka shude. A shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya baki daya za a iya cewa mutane sun fita yin zabe duk da cewa yankin ne ya ga tasku na Boko Haram.

Rahotanni daga jihohin Nasarawa da Benue da Plateau sun nuna cewar  ba'a sami fitowar jama'a ba kamar yadda ake tsammani a zaben. Wakilin mu Abdullahi Maidawa Kurgwi, ya ce a jihar Benue wasu 'yan ta'adda dauke da bindigogi sun kone kayayyakin zabe a wasu wurare cikin jihar. A can yankin Kudu maso Kudancin Najeriya kuwa misali a jihar Rivers zaben ya gudana lafiya sai dai mutane da dama sun yi zamansu a gida don gudun hargitsi kamar yadda wakilinmu Muhammad Bello ya rawaito mana.

Tuni aka shiga tattara sakamakon zabukan a yawancin jihohin da aka yi zaben na gwamnoni da 'yan majalisar jihohinsu a Najeriyar. Zaben da kungiyoyi na sakai ke cewa an yi lafiya.