Maganin coronavirus na gargajiya
May 14, 2020Kasashen Indiya da Chaina na daga cikin kasashen da al'ummarsu suka yi na'am da maganin gargajiyar. Kwatsam kuma sai kasashen Afirka suka fara ikirarin samar da magungunan gargajiyar domin yakar annobar cutar coronavirus din. Kasashen Najeriya da Ghana ma dai, al'ummarsu sun amince da batun maganin gargajiyar, inda tuni ma kungiyar masu maganin gargajiya ta Ghana, ta mika maganin da 'ya'yan kungiyar suka harhada ga gwamnatin kasar, da nufin yakar coronavirus din.
Ba girin-girin ba......
Sai dai tun ba a je ko'ina ba bayan da wasu kasashen Afirka uku ciki har da Jamhuriyar Nijar, suka yi na'am da maganin Madagaskan na gargajiya har ma suka saya, sai kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ta sanya kafa ta yi fatali da wannan magani. A cewarta babu wani binciken masana kimiyyar magunguna da ya tabbatar da sahihanci da ma ingancinsa, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi gargadin yin amfani da duk wani magani da masana ba su tantance ba.