1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaNijar

Nijar: Yaki da shan shisha da kayan maye

Gazali Abdou Tasawa LMJ
July 4, 2024

Hukumar 'yan sanda mai kula da kare tarbiyya a Jamhuriyar Nijar, ta kaddamar da samame a shagunan sayarwa da kuma shan tabar shisha a Yamai babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/4hsGq
Jamhuriyar Nijar | Samame | Shisha | Matasa
Illolin shan shisha a tsakanin matasaHoto: picture alliance/dpa

'Yan sanda sun kwace daruruwan kuttu da bututun shan shishar, a kokarin yaki da shaye-shaye wadanda ke taimaka wa wajen gurbata tarbiyyar jama'a musamman matasa tare da saka su aikata muggan ayyuka. 'Yan sandan shake a cikin motici bakwai, sun kuma kaddamar da samamen nasu a gidajen giya da otel-otel da wuraren taruwar matasa da ma na shakatawa. Babbar kwamishiniyar 'yan sanda kana shugabar sashen kula da tarbiyya na kasa Zouera Haousseize ta bayyana cewa, sun fahimci matsa na saka wasu muggan kwayoyi har ma da giya a  cikin shishar. A cewarta wannan ne ya sanya suka yi hobbasa, domin ceton rayuwar matasan da ma ta al'umma.

Illolin da ke tattare da shan shisha

Lokacin wannan samame dai, 'yan sanda sun kuma yi nasarar kama tabar wiwi da sauran haramtattun kayan maye da ma wasu daga cikin masu sana'ar sayar da shishar. To sai dai wasu al'ummar Nijar din na ganin akwai bukatar hukunta masu shigo da shishar da ma kayan shanta kasar, idan ana son matakin 'yan sandan ya yi tasiri musamman ga matsan da take wa illa. Yanzu haka dai a jerin samamen da hukumar 'yan sandan mai kula da tarbiyya ta kai na kamen shisha a Yamai, ta yi nasarar kama kuttun shishar sama da 5000 a cikin kasa da watanni shida.