Yakin Biafra: Wanda ya yi fama da yunwa
Bai cika shekara biyu lokacin da aka fara yakin Biafra ba. Amma Theophilus Chukwuemeka Amadi ya yi fama 'yunwa lokacin yakin basasa na Najeriya shekaru 50 da suka wuce, ya bayyana mummunan hali da suka samu kansu a ciki.
Shekaru biyu da rabi na yakin basasa
Yakin basasa ya barke a Kudu maso gabashin Najeriya tsakanin 1967 zuwa 1970. Wani bangare na kasar ya ayyana 'yancin kansa a karkashin sunan Biafra, wanda ya sa gwamnatin killace yankin gaba daya. An kiyasta cewa mutane miliyan biyu sun yi fama da matsananciyar yunwa. Theophilus Chukwuemeka Amadi ya tsira - saboda yaran kauyensu sun rika kama kadangare domin shi ya zama abincinsu.
'Ya'yan Biafra: Hotunan yunwa
Amadi yana daya daga cikin yaran da hotunansu a wancan lokacin suka mamaye duniya: Sun rame amma duk da haka suna da genden ciki. Sun kamu da cutar da ake kiranta Kwashiorkor. Ana kamuwa da ita sakamakon karancin abinci mai gina jiki. "Idan mutum ya kamu da Kwashiorkor, a yawanci lokuta alama ce ta kusantar mutuwa," in ji Amadi, wanda dan uwansa bai tsira daga cutar ba.
An samu hadin kai mai karfi
Hadin kai tsakanin iyali ya kasance wani abu mai daraja: "Lokacin da na yi rashin lafiya, kowa ya damu. Kowane mutum yana son tabbatar da cewa wannan yaron ya rayu," in ji Amadi. Dukkanin 'yan uwa da dangi sun goyi bayan mahaifiyarsa (a hannun dama a hoto) don ƙaramin Amadi ya sami taimakon da ya kamata.
"Sun bani damar rayuwa"
Amadi ya sami damar yin bikin zagayowar ranar haihuwarsa na shida a 1971, shekara guda bayan yakin, saboda kungiyoyin agaji sun kula da lafiyarsa tare da taimakawa da abinci." Idan da masu taimakon ba su kasance a wurin ba, da ban tsira ba. Sun sadaukar da lokacinsu. Sun sadaukar da dukiyoyinsu, "in ji Amadi. Ya zame ma wata kungiya mai zaman kanta mai suna Save the Children abin misali.
Tunawa da abin da ya faru
Amadi ya karanci ilimin addini kuma yanzu yana aiki a gidan adana kayan tarihin yaki a Umuahia. Yayin yakin, garin ya kasance na dan lokaci babban birnin kasar Biafra. Dan shekaru 54 da haihuwa ya ce yana farin ciki lokacin da wadanda suka tsira daga yaki suka je gidan adana kayan tarihi: "Suna taimakawa wajen tunatar da illar yakin ga wadanda ba su gani ba."
Hotunan wadanda rikicin ya shafa Berichte eines Zeitzeugen
Lokacin da yake jagorantar baki don baje kolin abin da ya faru, idan ya iso kan hotunan wadanda yakin basasan Biafra ya shafa, yana gaya musu cewa shi da kansa ya sha wahala daga cutar Kwashiorkor a lokacin yakin shekaru 50 da suka gabata.
Abubuwan tunawa masu mahimmanci
Duk da cewa Amadi karamin yaro ne a lokacin yakin, amma yana iya tuna wasu abubuwa da suka faru: "Zan iya tuna yadda mutane suka gudu, suna neman wurin boyewa daga hare-hare ta sama, ko boye wa sojoji. Kuma babu abinci." Wannan hoton yana nuna garin Umuahia a shekarar 1969, jim kadan bayan sojojin Najeriya suka killace garin.
samar da makoma mai kyau
Yau Amadi yana da 'ya'ya hudu. Yana son samar da rayuwa mafi kyau a gareshi da makoma ta gari ga sauran yara, tare da tunawa da mummunan babi na tarihin tarayyar Najeriya.