1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Merkel a Aachen

Binta Aliyu Zurmi
September 25, 2021

A shirye-shiryen karshe na tunkarar babban zaben kasar Jamus, a ranar Asabar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ziyarci mahaifar dan takarar jam'iyyar CDU Armin Laschet.

https://p.dw.com/p/40rVi
Wahlkampf CDU | Angela Merkel und Armin Laschet
Hoto: Martin Meissner/AP/picture alliance

Armin Laschet mai shekaru 60 da haihuwa da Merkel ke fatan ya gajeta na karawa da abokin takararsa na jam'iyyar SPD Olaf Schulz, duk da cewar Merkel na kokarin janyewa daga siyasa bayan kwashe shekaru ana damawa da ita amma an ganta a garuruwa da dama tana tallata dan takararta. 

Sa'o'i 24 kafin zaben, Merkel ta karkare yakin neman zaben da ziyarta birnin Aachen da ke yammacin Jamus, mahaifa ga dan takararta Armin Laschet inda ta jaddadawa al'ummar wannan birni. Merkel ta ce wannan zabe na da matukar muhimmanci, ta kuma kara da bukatar al'umma da su zabi  dan takararta a gobe.

Da sanyin safiyar Lahadi ne za a bude rumfunan zabe don ba wa jama'a dama su kada kuri'arsu kuma za a rufe rumfunan da misalin karfe 6 na yamma.