Siyasar Najeriya: Hade kan 'yan adawa
December 7, 2023Kama daga PDP da ke jagorantar adawa a cikin Tarayyar Najeriyar ya zuwa SDP ko bayan NNPP da YPP dai, kimanin jam'iyyu bakwai da ke da wakilci a cikin majalisun dokokin kasar suka kaddamar da sabon kawancen da suke fatan ya sauya fagen siyasar Najeriyar a nan gaba. Tun cikin watan Nuwambar da ya shude madugun adawar kasar Atiku Abubakar ya ce akwai bukatar su hade wuri guda, domin tunkarar masu tsintsiyar da ke dada mamaye fagen siyasar kasar yanzu haka.
Karin Bayani: Atiku: Sai mun tabbatar da gaskiya a kotun koli
Sabon kawancen da aka yi wa lakabi da Coalition of Concern Political Parties dai, na zaman irinsa na farko da ke da burin tankwabar da damar mulkin daga hannun APC. Duk da cewa dai jam'iyyun ba su kai ga ayyan hadewa wuri guda ko kuma irin tsarin da kawancen ya ke shirin yabi ba, daga dukkan alamu sabon shirin na zaman martini ga zargin hannu da kafar masu tsintsiyar cikin shari'un zaben da suka tayar da hankali cikin kasar. Shugaban jam'iyyar NNPP na kasa Abba Kawu Ali ya nunar da cewa, idon masu tsintsiyar na rufe a kokarin neman zaben shekara ta 2027.
Kwace zuwa gidan APC ko kuma raki cikin gida na adawa dai, sai da ta kai ga adawar hadawa wuri guda a shekara ta 2014 kafin iya kai wa ga kare fatan PDP na share 60 bisa kujerar mulki. Ana dai kallon batun hadewa wuri guda na zaman na kan gaba a kokarin masu adawar, maimakon kawancen da ke iya rushewa a lokaci kankane. To sai dai kuma haduwar a fadar Shehu Musa Gabam da ke zaman shugaban jam'iyyar SDP na kasa, ba zai haifar da natija mai kyau ga kokarin gina tsarin dimukuraddiyar Najeriyar ba.
Karin Bayani: Najeriya: Tsugune ba ta kare ba kan zabe
Kawance maimakon batu na hadaka dai, sabuwar dabarar ta adawa da ke zuwa watanni shida da kafa gwamnati a Najeriyar na iya kai wa ya zuwa murde wuyan cikin gidan na adawa a bangaren APC da ke da daurin gindin alkalai da jami'an tsaro a tunanin Faruk BB faruk da ke sharhi cikin batun na siyasa. Abun jira a gani dai na zaman tasirin gwagwarmayar ta adawar da ke da fatan sauya da dama a cikin tsarin mai karfi sai Allah.