SiyasaArmeniya
Zanga-zangar 'yan Armeniya mazauna Turai
October 1, 2023Talla
Masu aiko da rahotanni sun ce adadin masu zanga-zangar ya kai mutum dubu 10 wadanda ke dauke da alluna da kuma tutocin Armeniya suna rera kalaman Allah wadai da mahukutan Turai kan rashin daukar mataki kan Azerbaijan bayan aikata abin da suka kira cin zarafin Armeniyawan Nagorno-Karabakh.
Karin bayani: Nagorno-Karabakh: Al'umma na neman agaji
Wasu majiyoyi sun ce tsohon ministan harkokin wajen Faransa Bernard Kouchner shi ma ya halarci zanga-zangar ta Brussels domin karfafa gwiwa ga 'yan Armeniya a cikin wannan yanayi. Kamfalin dillancin labaran Faransa AFP ya ruwaito tsohon ministan na cewa dole ne kungiyar tarayyar Turai ta shiga tsakanin a rikicin tare da sa ido kan iyakokin Armeniya saboda abin da ka iya zuwa nan gaba.