Shugaban Turkiyya zai gana da takwaransa na Azerbaijan
September 24, 2023Sanarwar da mahukuntan Ankara suka fidda na nuni da cewar babban batun da shugabannin biyu za su tattauna a kai shi ne batun rikicin yankin Nagarno-Karabakh.
Gwamnatin Turkiyya ta jima tana goyon bayan sojojin Azerbaijan, musamman ma a wannan sabon rikicin.
A daya hannun kuwa al'ummar Armeniya ne suka bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta hanzarta tura dakarun wanzar da zaman lafiya yankinsu domin saka ido a kan yancinsu da ma tabbatar musu da tsaro, bayan yarjejeniyar tsagaita wuta da ma jingine makamai da aka fara a ranar Juma'ar da ta gabata.
Wannan na zuwa ne bayan da a jiya Asabar gwamnatin kasar Azerbaijan ta yi wa duniya alkawarin kiyaye hakkokin Armeniyawa mazauna yankin Nagorno-Karabakh, yanki da takaddama ta yi zafi a tsakaninta da kasar Armeniya.