Najeriya: 'Yan bindiga sun kashe mutum 17
May 4, 2021Talla
Wani mai magana da yawun gwamnatin jihar ya tabbatar wa manema labaran harin, wanda yake zargin fulani makiyaya da aikatawa kan mazauna yankunan Tijime da Achabo da ke gabashin jihar, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mata da kananan yara.
Ba tun yau ba dai ake samun takun saka tsakanin makiyaya da manoman yankin, tun bayan da gwamnatin jihar ta dauki matakin hana kiwo mai cike da cece-kuce.