1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sace mutane 150 a Zamfara

Abdul-raheem Hassan
November 25, 2023

Masu garkuwa da mutane sun kashe mutum daya sun kuma dauke akalla mutane 150 ciki har da mata da yara a kauyuka hudu na Jihar Zamafara da ke Najeriya.

https://p.dw.com/p/4ZRSg
Samfurin makaman da masu garkuwa ke amfani da su a NajeriyaHoto: Stefan Heunis/AFP/Getty Images

Mazauna kauyukan hudu da aka yi garkuwa da mutanensu sun tabbatar da cewa maharan sun afkawa karamar hukumar Maru kan babura. Dankandai Musa, wani mazaunin daya daga cikin kauyukan ya ce ya labe ba tare da an gane shi ba a lokacin da aka kawo harin, amma an kwashe mutanen gidansa 20.

"Na yi nasarar tserewa ne bayan sun sake tattara mu da kuma mutanen wasu kauyuka uku da aka kai harin,” inji shi. Ya kara da cewa "Na gudu a lokacin da suke jan mu zuwa daji."

Wani hakimin kauyen ya ce Lawali Damana, shi ne shugaban kungiyar da ta kai harin.

‘Dan bindigar ya bukaci naira miliyan 100 ($119,000) daga hannun mazuna kauyukan a matsayin ramuwar gayya, bayan sojojin Najeriya sun kashe hudu daga cikin mutanensa.

Garkuwa don neman kudin fansa ya zama ruwan dare a arewacin Najeriya a baya-bayan nan inda suke kwashe mutane a gidajensu da makaratu. Har yanzu matakan sabuwar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ba su yi wani cikakken tasiri kan magance matsalar tsaron ba tukun da ke addabar yankunan arewacin Najeriya ba.