1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijira a Najeriya da zaben 2015

Uwais Abubakr IdrissDecember 3, 2014

Ana nuna damuwar cewa mutanen da suka rasa muhallansu a dalilin hare-hare na kungiyar Boko Haram, ba za su iya gudanar da zabe a 2015 ba.

https://p.dw.com/p/1Dyv0
Nigeria Flüchtlinge in Maiduguri
Hoto: picture alliance/AP Photo

Kara munin da kai hare-hare na ta'addanci ke yi musamman a yankin arewa maso gabashin Najeriya na ci gaba da tilasta wa dubun dubatan mutanen barin muhallansu a yanayi babu shiri, domin kuwa hukumar kai daukin gaggawa ta kiyasta yawan irin wadannan mutane da cewa ya kai dubu 800, yayinda wasu kungiyoyi ke cewa sun zarta miliyan daya.

Makomar 'yan gudun hijira a zaben Najeriya

Wannan ya sanya nuna damuwa a kan makomar samun damar jefa kuri'a ga duban mutanen da suka rasa muhallan nasu abinda ya sanya hukumar zaben Najeriyar da ma kungiyoyi masu zaman kansu daga 'yar yatsa. Amma a yayin da ake wannan batu ga wadanda abin ya shafa na tunanen wani batu na daban ne kamar yadda shugaban al'ummar Chibok da ke gudun hijira a yankin Abuja har ma da jihar Nasarawa Hosea Tsambido Habana ya bayyana.

"To in ma an ce za a kai rumfar zabe a wajen masu gudun hijirar in dai ba an sasu dole ne ba, ba ma za su fita zaben ba, domin mutane suna ganin mene ne ma amfani zaben. Ko da yake da zaben ne ake zaben wakilan da za su iya kawo mana zaman lafiya, amma a Najeriya kana tsamanin kuri'a ne ake zaba. Ai ba zaben kuri'a ne ba, domin wadanda suke gudun hujira ba cikakken bayani a kansu, an samu hanyar da za a yi magudi."

Wahlen Nigeria Attahiru Jega
Hoto: AP

Duk da cewa hukumar zaben Najeriya ce ta daga batun damar jefa kuri'a ga mutanen da suka rasa muhallansu amma ga shugaban hukumar Farfesa Attahiru Jega na mai bayyanin cewa in dai batun magudi ne ta kowace hanya babu shi a zaben na 2015.

"In dai wani shiri ake kokari a yi a magudi in Allah ya yarda ba za a samu nasara ba, saboda tanajin da muka yi da shiri na tabbatar da cewa akwai ingantacciyar rijista. Don haka ina kokari in yi amfani da wannan dama cewa sai an fa yi hakuri da al'ammuran da suka shafi zabe."

Tuni majalisar datawan Najeriyar ta fara daukar mataki bisa kudurin da aka gabatar mata a kan wannan batu, musamman yadda mutanen da suka rasa muhallan nasu suka watsu kama daga jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa zuwa sassan Najeriya daban daban.

Kudurin yi wa dokar zabe kwaskwarima

Flüchtlingslager in Bama, Nigeria
Hoto: Reuters/S.Ini

Sanata Ali Ndume shi ne ya gabatar da kudurin yiwa dokar zaben Najeriyar gyaran fuska domin bai wa mutanen da suka rasa muhallansu daman yin zabe a inda suke na kuma tambaye shi ko ina aka kwana ga wannan aiki mai muhimmanci?

"Dama ka san wannan aiki akwai tsari da zai bi, daga kan Gwoza yanzu mafi yawan mutane da suke wurin sun yi gudun hijira suna Maiduguri, amma akwai kalilan watakila a wurare jifa-jifa. To wuraren da mutanen suke idan sun san cewa a Maiduguri za a yi zaben to in lokacin zaben ya zo can Maiduguri za su je inda mutanensu ke gudun hijira don su kada kuri'arsu. Sauye-sauyen da na kawo ai don ya bada dama a dauki akwatin zabe daga wurin da yake inda ba za a iya zuwa ba, zuwa wuraren da mutanen suke gudun hijira don su kada kuri'arsu."

Amma ga Barrister Mainasara Umar masani a harkar shari'a ya ce dole ne fa a san matakin da za a dauka saboda illar da ke tattare da hana su yin zabe a 2015.

Abin jira a gani shi ne ko majalisar datawa za ta iya kaiwa ga kammala aikin gyaran fuska ga wannan doka domin kauce wa hana dubban mutanen da rigingimu suka rabasu da muhallansu gudanar da zabe a 2015.