1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chadi ta karbi 'yan gudun hijira daga Sudan

Blaise Dariustone | Mohamed Tidjani Hassane SB/MAB
July 18, 2023

Yayin da rikicin Sudan ke kara kamari, kungiyoyin agaji a Chadi sun bayyana damuwa kan karancin kayan kula da dubban 'yan gudun hijira da ke ci gaba da kwarara kasar domin neman mafaka.

https://p.dw.com/p/4U4q2
Chadi I 'Yan gudun hijira na Sudan da suke tsere zuwa kasar Chadi
'Yan gudun hijira na Sudan da suke tsere zuwa kasar ChadiHoto: Blaise Dariustone/DW

Yayin da rikicin Sudan ke kara kamari, kungiyoyin agaji a Chadi sun bayyana damuwa kan karacin kayan kula da dubban 'yan gudun hijira da ke ci gaba da kwarara kasar domin neman mafaka. A cewar kungiyoyin tsakanin watan Mayu da na Yuni masu tserewa rikicin da suka hadar da 'yan Chadi da 'yan Sudan din ya haura mutum dubu 200. DW ta kai ziyara a daya daga cikin sansanonin da aka tsugunar da 'yan gudun hijirar don duba halin da suke ciki.

Karin Bayani: Rikicin Sudan na ci gaba da tayar da hankali

 cahdi I 'Yan gudun hijira na Sudan da suke tsere zuwa kasar Chadi
'Yan gudun hijira na Sudan da suke tsere zuwa kasar ChadiHoto: Mahamat Ramadane/REUTERS

A sansanin 'yan gudun hijira na garin Adre hedkwatar yankin Assounga da ke iyakar Chadi da Sudan. Sama da 'yan gudun hijira dubu 65 galibi 'yan Sudan da kuma 'yan asalin Chadi da suka tsere wa rikicin da ya barke yau da watanni hudu ne ke a tsugune a wannan sansani karkashin kulawar kungiyoyin agaji na kasa da kasa. Wadannan bayun Allah da ba su ji ba su gani ba, galibi mata da kananan yara na rayuwa a sasanin karkashin runfuna na tanti da kuma na yadi duk irin tsananin ranar da ake wanda wasu lokutta ke haura maki 46 a ma'aunin celcuis.

A kullum bakin 'yan gudun hijira na karuwa a sansanin lamarin da fara gagarar kungiyoyin da ke ba su kulawa. Laura Lo Carstro jakadiyar hukumar koli ta Majalisar Dinkin Duniya mai kula da 'yan gudun hijira a Chadi ta bayyana damuwa kan karancin kayan agaji domin bayar da kulawar da ta dace ga 'yan gudun hijirar da a kullu yaumin adadinsu ke karuwa.

Chadi I 'Yan gudun hijira na Sudan da suke tsere zuwa kasar Chadi
'Yan gudun hijira na Sudan da suke tsere zuwa kasar ChadiHoto: Gueipeur Denis Sassou/AFP

Kawo yanzu alkaluma sun tabbatar da cewar sama da mutune dubu 192 ne  suka shiga Tchadi tun bayan barkewar rikicin na Sudan, adadin da ake sa ran na iya haura mutum dubu 250 kafin karshen wannan shekara. A yayin wata ziyara da jakadiyar Majalisar Dinkin Duniya da ke Chadi ta kai wa sansanin na garin Adre, Violette Kakyomya ta nuna kaduwa kan halin kuncin da ta iske 'yan gudun hijirar a ciki. Wannan ne ma ya kai jami'ar ga cewa ya kamata a gagauta kawo karshen rikicin na Sudan, wannan kawo yanzu da yi ajalin mutane sama da dubu uku.

Dama dai ko baya ga wadannan sabin 'yan gudun hijirar Sudan da ke kwarara Tchadi mai makwabtaka, da akwai karin wadansu sama da dubu 400 da ke tsugune a kasar tun bayan barkewar yakin basasan Darfur wanda ya daidaita yakin tsakanin shekarun 2003 izuwa 2008.