'Yan gudun hijira sun samu sabbin gidaje a Borno
October 24, 2022Wannan mataki na samar da gidaje da hanyoyin rayuwa ya kasance wani bangare na sake farfado da shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya wanda rikicin Boko Haram da aka kwashe sama da shekaru 13 a na fama da shi ya daidaita. An raba gidajen ga wadanda suka rasa ‘yan uwansu da gidajensu da dukiyoyinsu, lamarin da ya kai su ga yin gudun hijira zuwa wuraren da ke zama tudun na tsira,
A wani taro da aka gudanar domin Kaddamar da wadannan gidaje, an sanar da raba musu dabbobi da za su kiwata domin dogaro da kai. Jakadar kasar Jamus Annett Günther da ta halarci rabon gidajen ta jinjina wa al'ummar Ngarannam da ke karamar hukumar Mafa saboda jajircewarsu na komawa garinsu don sake sabuwar rayuwa.
Günther ta ce: "Jajircewa da kuka yi wajen yakar tsoro da aka samu tare da dawowa garuruwanku na bukatar na mijin kokari. Kuma da kyakkyawan nufi na sake farfado da garuruwanku abu ne da ke nuna cewa za a iya kawo karshen wannan matsala ta ta'addanci tare da gina sabuwar rayuwa, wadda za ta samar da wasu damammaki musamman na abun da kuka gani a baya na ta'addancin Boko haram da sauran ‘yan ta'adda."
Zulum ya nemi goyon bayan al'umma wajen raya Borno
Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce samar da irin wadannan gidaje a wannan lokaci, wata manumaniya ce kan kokarin farfado da shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya.Ya ce: "Abun da muka kaddamar yau ya nuna misalin nasararorin da za mu iya cimmawa idan mun hada kawunanmu musamman wajen mutunta shugabanci a jiha."
Wasu daga cikin wadanda su ka amfana da rabon gidajen sun yaba yadda aka cire musu kitse a wuta, kuma an ba su abun da za su farfado da rayuwarsu.
Hajiya Fulata, tsohuwar 'yar gudun hijira da ta samu gida, ta ce: " Na gode musu, na ji dadi. Da muna shan wahala a can, ga 'yunwa ga ba abinci, ga ba komai, muna shan wahala a Maiduguri amma yanzu sun kawo mu gida."
Masu fashin baki kan harkokin yau da kullum sun yi fatan a samar da isassun matakai tsaro a yankuna da aka samar da wadannan gidaje domin kare al'umma daga hare-haren mayakan Boko Haram wadanda ke neman dawo da ayyukansu a wannan lokaci.