1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An yi garkuwa da daruruwan mutane a arewacin Najeriya

Mohammad Nasiru Awal MAB
August 19, 2020

Da yammacin ranar Talata 'yan ta'addan da ke da alaka da kungiyar ISWAP suka yi wa garin Kukawa diran mikiya suka yi garkuwa da mutane da ba su dade da komawa garin ba.

https://p.dw.com/p/3hC76
Nigeria Islmischer Staat in West Afrika ISWAP Truck
Hoto: Getty Images/AFP/A. Marte

Wasu 'yan Jihadi da ke mubaya'a da kungiyar IS, sun yi garkuwa da daruruwan mutane a garin Kukawa da ke Arewa maso gabashin Najeriya, a cewar majiyoyin soji da mazauna yankin a wannan Laraba.

Babakura Kolo da ke zama shugaban 'yan sa-kai na yankin ya fada wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa da yammacin ranar Talata 'yan ta'addan kungiyar IS ta yankin yammacin Afirka wato ISWAP sun yi wa garin na Kukawa diran mikiya suka yi garkuwa da mutane da ba su dade da komawa garin ba, bayan sun shafe kusan shekaru biyu a sansanonin 'yan gudun hijira.

Wakilinmu a Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno, Al-Amin Suleiman Mohammad shi ma ya tabbatar da labarin inda ya kara da cewa 'yan Jihadin sun kakkafa tutocinsu a garin.

A cikin manyan motoci 22 ne dai 'yan ta'addan suka shiga garin da yammacin ranar Talata, inda suka yi mummunan gumurzu da sojoji da ke gadin garin.

A ranar 2 ga watan nan na Agusta sojoji suka raka mazauna garin komawa gida bisa umarnin hukumomin jihar Borno.