'Yan kasuwan Nijar sun damu kan harajin masarufi
January 3, 2024A watan Oktoban 2023 ne gwamnatin milkin sojan Nijar ta rage 25% na harajin wasu kayyakin masarufi guda 10 da aka fi amfani da su a kasar da suka hada da shinkafa da taliya da man girki da garin fulawa da madara da sauransu. fadar mulkin ta Niamey ta ce matakin zai shafe watanni uku ywanda ya kawo karshe a ranar 31 ga watan Disamba, 2023. A kan haka ne gwamnatin ta sake maido da harajin a kan wadannan kayayyaki. Sai dai Alhaji Sani Chekaraou, shugaban kungiyar manyan ‘yan kasuwa masu shigo da kaya daga waje ya bukaci gwamnati ta janye matakin dawo da haraji.
Karin bayani:Matslar karancin shinkafa na kara kamari a Nijar
Su ma kungiyoyin yaki da tsadar rayuwa da fafutukar kare hakkin masu sayan kayayyaki sun bayyana damuwarsu a game da yiwuwar karuwar farashin kaya a sakamakon maido da harajin, kamar yadda Mamane Nouri, da ke shugabatar kungiyar ADDC- Wadata, daya daga cikin wadannan kungiyoyi. Shi kuwa Itinikar Alassan wani matashin dan siyasa a Nijar, cewa ya yi matakin da gwamnatin mulkin sojan ta dauka bai ba shi mamaki ba.
karin bayaniJamhuriyar Benin ta sake bude kofofinta ga 'yan Nijar:
Shugaban babbar kungiyar ‘yan kasuwan Nijar ya gargadi 'yan kasuwa da su kauce wa kara kudin kayan ajiya da ke a kasa, kana ya sha alwashin tinkarar mahukunta domin samar da wata mafita ta dabam kan wannan batu na haraji.