1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ana fama da karancin shinkafa a Jamhuriyar Nijar

Larwana Malam Hami Abdoulaye Mamane
October 3, 2023

A wani mataki na rage radadin tsadar rayuwa da takunkuman kungiyoyin ECOWAS da UEMOA, gwamnatin Nijar ta zabge kaso 25 cikin 100 na kudin fito ga 'yan kasuwa, amma kuma duk da hakan shinkafa ta yi karanci

https://p.dw.com/p/4X4yG
Shinkafa na daga cikin muhimman cimakar da masu dan hali ke amfani da ita a Nijar
Shinkafa na daga cikin muhimman cimakar da masu dan hali ke amfani da ita a NijarHoto: picture-alliance/dpa

Takunkuman da kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afirka ECOWAS/CEDEAO da na kungiyar kasashen da ke amfani da kudin bai daya na UEMOA suka kakaba wa Nijar na ci gaba da yin tasiri kan wasu nau'ukan kayan abinci da na bukatun yau da kullum musamman ma shinkafa.

Duk da matakin rage kaso 25 cikin 100 na kudin fito da gwamnatin mulkin sojin Nijar ta yi wa 'yan kasuwa, har yanzu ana fuskantar karancin cimaka da sauran kayayakin bukatun yau da kullum a wasu sassan na jamhuriyar Nijar.

Farashin shinkafa guda daga cikin cimakar da aka fi amfani da ita a manyan birane ya karu da kaso fiye da 15 cikin 100 na adadin kudin da ake sayar da buhun shinkafar a gabanin sojoji su yi juyin mulki.

Karin Bayani:  Cece-kuce kan Jamhuriyar Nijar a Majalisar Dinkin Duniya

A kokarin magance matsalar shugaban mulkin sojan Nijar Janar Abdourahmane Tchiani ya gana da 'yan kasuwa masu shigo da kayan abinci, ya roke su da su tausayawa masu karamin karfi a cikin halin da aka shiga na kaunkumai daga kasashen duniya, ya tabbatar da musu da tsaro ta hanyar kare kayan da suke shigowa da su idan sun bi ta kasar Burkina Faso.

Gwamnatin mulkin soja ta kuma kafa kwamitin na musamman da ke bibiyar 'yan kasuwa bayan sun gana da shugaban kasa, burinsa shi ne na duba halin da kayan abinci suke ciki a kasuwanni, sai dai duk da haka farashin shinkafar bai ragu ba.

'Yan kasuwa sun koka da cewa akwai dalilai da suka yi sanadiyar tashin farashin kayan abincin musamman ma na shinkafa, kamar tsadarta daga kasashen waje da takunkumin hana fitar da ita da wasu manyan kasashe manoman shinkafa suka gindaya, ga kuma takunkuman karayar tattalin arziki da suka kara haífar da matsaloli wajen fiton kayayyaki zuwa Nijar.

Ana fama da karancin shinkafa a manyan biranen Jamhuriyar Nijar
Ana fama da karancin shinkafa a manyan biranen Jamhuriyar NijarHoto: picture-alliance/BSIP

Karin Bayani:  Tsohon Shugaba Issoufou ya juya wa Bazoum baya

Shugabannin kungiyar 'yan kasuwa a Nijar kamar su Alhaji Sama'ila Hatimou sun bayyana cewa "'yan kasuwar Nijar sun yi kokari sun rike farashi ba tare da sun kara ba, ragowar shinkafar da ke da saukin kudi da ke aje a shagunan manyan 'yan kasuwa ta kusa karewa."

A baya-bayan nan kasar Indiya ta haramta fitar da shinkafa a kasashen ketare, lamarin da ya shafi kasashe da dama ciki har da Jamhuriyar Nijar

Alumma na cikin wani mawuyacin hali na tsadar kayan abinci tun bayan juyin mulki, wasu da dama sun bukaci a kafa kwamitin da zai rika tsayar da farashin kayan abinci a wata ganawar da suka yi da jami'an Nijar

Ragowar kayan abinci kamar Masara Gero da Dawa da Wake duk sun fara tashi, duk da yake ba sosai ake amfani da ragowar cimakar ba kamar shinkafa.