1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan matan Chibok 82 sun hadu da iyayan su

Salissou Boukari
May 20, 2017

A wannan Asabar din ce a Abuja babban birnin Tarayyar Najeriya, iyayen 'yan matan Chibok guda 82 da aka samu ceto su daga hanun Boko Haram suka gana da ‘ya'yan na su a wani kwarya-kwaryan biki da aka gudanar.

https://p.dw.com/p/2dIlg
Nigeria - Heimkehr der Chibok Mädchen
'Yan matan Chibok 82 sun gana da iyayan suHoto: picture-alliance/dpa/AP/O. Gbemiga

Iyaye da dama dai sun bayyana murna su a fili ta hanyar kade-kade da raye-raye da sake haduwa da 'ya'yan  su musamman inda suka tuna irin yadda suke zaune da su kafin sace su da Kungiyar Boko ta yi. Daya daga cikin iyayen mai suna Rebecca Ntaki da ta ga diyar ta Hauwa na cike da murna. Gwamnatin Najeriyar dai ta yi alakwarin ci gaba da kula da lafiyar yaran musamman inda kwarrau  za su ci gaba da ba su shawararwari domin kwantar ma su da hankali saboda irin rayuwar da suka samu kansu a ciki.