1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan matan Chibok: Alhinin cika shekaru 10 da sace su

April 10, 2024

A wannan wata na Afrilu ake cika shekaru 10 da sace daliban Makarantar 'yan mata ta Chibok da ke jihar Borno a Najeriya, da labarin sace daliban ya mamaye manyan labaran jaridun kasashen duniya a ranar 14 ga watan.

https://p.dw.com/p/4ed1b
Wasu daga cikin 'yan matan Chibok da aka kubutar a 2017 a Najeriya
Wasu daga cikin 'yan matan Chibok da aka kubutar a 2017 a NajeriyaHoto: Sunday Aghaeze/AFP

Jimamin sace daliban Chibok na zuwa ne a 'yan makonni da sace dalibai kusan sau biyu a kasar a Najeriyar ciki har da daliban Kuriga a jihar Kaduna, a salon satar da aka yiwa daliban Chibok a shekaru goman da suka gabata.

Karin bayani: Boko Haram ta aura wa kanta sama da 'yan matan Chibok 20

'Yan bindiga da masu ikrarin jihadi na amfani da matasar tsaron Najeriya wajen sace daliban makarantu a sassan kasar musamman a yankin arewacin kasar.

Karin bayani:Shekaru 7 da sace 'yan matan Chibok 

A shekara ta 2000 'yan bindiga na kai farmaki ga ma'aikatan da ke aikin hakar mai da iskar gas a yankin Niger Delta, wanda daga bisani masu ikrarin jihadi suka kaddamar da hare-hare a shiyyar arewa maso gabas. Babu tabbacin alkaluman mutanen da ake sacewa a Najeriya kasancewar lamarin ya zama ruwan dare gama duniya da kuma watsi da lamarin da kafafen yada labaran kasa-da-kasa sukayi.