'Yan matan Chibok sun gana da Buhari
May 7, 2017Mahukuntan Najeriya sun tabbabar da karbo 'yan mata 'yan makarantar Chibok 82 daga hannun Kungiyar Boko Haram a jiya Asabar daga cikin jerin 'yan matan kusan 200 da kungiyar ta sace shekaru uku da suka gabata. Wata majiyar sojin kasar ce ta fara sanar da wannan labari kafin daga bisani shugaba Buhari ya tabbatar da hakan a saman shafin sa na Twitter inda ya ce an karbo 'yan matan ne a karkashin wani shiri na musaya da wasu kwamandojin Boko Haram da mahukuntan Najeriyar ke tsare da su.
Majiyar sojin Najeriyar ta sanar da cewar da misalin karfe biyar da rabi na yammacin jiya ne wasu motoci suka je suka dauko 'yan matan daga cikin wani daji da kungiyar ta ajiye su, inda daga nan ne aka dauko su zuwa garin Banki na kan iyakar da Kamaru, kuma yanzu haka an ba su mafaka a wani sansanin sojoji kafin zuwa wannan rana ta Lahadi inda wani jirgi zai dauko su zuwa Maiduguri, bayan sun gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.