'Yan matan Chibok za su koma gida
August 19, 2017Gwamnatin Najeriya, ta ce sama da 'yan matan makarantar Chibok 100 da suka kubuta daga hannun Boko Haram din nan, suna gab da komawa harkokinsu na rayuwa yadda suka saba a baya. Ministar harkokin mata ta Najeriyar ce ta sanar da hakan a wata ganawar da ta yi da manema labarai, tana mai tabbatar da cewa 'yan matan su 106 sun warke tsaf, kuma za su mika su da iyayensu, su kuma koma makaranta.
Su dai wadannan 'yan mata na Chibok sun sami kulawa ta musamman a hannun mahukuntan Abuja, bayan sako su da mayakan Boko Haram suka yi. Cikin watan Mayun bana ne kungiyar ta Boko Haram ta sako 82, wasu 24 ma suka kubuta a bara. Bayan 'yan matan na Chibok kimanin 100 suka saura yanzu a hannun Boko Haram, akwai ma wasu daruruwan jama'a mata da maza da kungiyar ke garkuwa da su.