1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Niger Delta sun ce ba a kula da su

June 20, 2017

Wasu mazauna jihohin Rivers da Bayelsa da Delta a Najeriya sun yi zanga-zanga bisa dalilai da suka ce sun hada da watsin da kamfanin mai na Agip ya yi da su ta fuskar samar da aiyyuka yi ga jama'a da ababan more rayuwa.

https://p.dw.com/p/2f2P5
Nigeria Niger-Delta Ölverschmutzung Kläger Eric Dooh
Hoto: picture-alliance/dpa/M. van Dijl

Tun san yin safiyar Talatar nan ce (20.06.2017) masu zanga-zangar suka tattaru a garin Rumolimeni da ke wajen birnin Fatakwal, fadar jihar Rivers don gudanar da zanga-zangarsu sai dai duk da cewar zanga-zangar ta lumana ce, wadnda suka shiryata sun zargi kamfanin na Agip da jijjibge jamian tsaro dauke da makamai inda kuma suka hana jama'a motsawa.

Guda daga cikin masu zanga-zangar mai suna Igoni Koko wanda ya fuskanci fushin jami'an tsaro ya ce ''sun (jami'an tsaro) yaga min kaya sannan sun kada ni cikin kwatami.'' Da ya ke tsokaci kan wannan lamari madugun masu zanga-zangar Clement Ada ya ce ba su ji dadin yadda aka hana su aiwatar da abinda suka so yi ba inda ya kara da cewar ''kamfanin Agip ya mayar da mu saniyar ware ta ko wane bangare. Muna bukatar da a hanzarta cire shugaban kamfanin kuma dole ne su martaba yarjejeniyoyin da ke tsakaninmmu na tallafawa rayuwar jama'a.''

Kamfanin na Agip dai da 'yan zanga-zangar suka zarga da assasa yawan matasa masu zaman kashe wando a yankin na Niger Delta ya hana kowa rabar harabar ofishinsa balle ma a ji ta bakinsa kan wannan lamari ba amma a share guda masu zanga-zangar sun ce za su cigaba da yin matsin lamba ga kamfanin har sai hakarsu ta kai ga cimma ruwa.