Abuja: 'Yan sanda sun mutu a rikicin Shi'a
August 25, 2024Rundunar 'yan sanda a Najeriya ta tabbatar da mutuwar jami'anta guda biyu wasu guda uku sun samu mumunar rauni tare da kona motocin 'yan sanda a wani rikici da ya barke tsakaninsu da 'yan Shi'a a Abuja babban birnin kasar.
"Haramtacciyar kungiyar ta kai hari a shingen bincike, suna dauke da adduna da wasu ababen fashewa da wukake,” inji mai magana da yawun ‘yan sandan Josephine Adeh a cikin wata sanarwa da ta fitar.
Rundunar ta ce an kama mutane da dama, inda kwamishinan 'yan sandan birnin Abuja CP Benneth C. Igweh, ya ce za a gurfanar da su a gaban kotu. Mabiya kungiyar IMN na gudanar da jerin gwano da suka saba yi na cika kwanaki 40 bayan Ashura.
Tun a shekarar 2019, gwamnatin Najeriya ta haramta kungiyar Shi'a ta IMN, bayan wata zanga-zangar neman a saki shugabanta Sheik Ibrahim El-Zakzaky da aka daure tun a shekarar 2015 zuwa 2021 bayan artabu da sojoji wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 300.