1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

'Yan sandan Faransa sun tsaurara tsaro a filin wasa na PSG

April 10, 2024

'Yan sandan Faransa sun kafa shingayen bincike a ciki da wajen birnin Paris musamman a Parc des Princes, sakamakon barazanar kai hari da kungiyar IS ta yi gabanin wasannin Olympic na bazara da za a gudanar a kasar.

https://p.dw.com/p/4edCA
Magoya bayan kungiyar PSG a Parc des Princes
Magoya bayan kungiyar PSG a Parc des PrincesHoto: Michel Euler/AP/picture alliance

A filin wasan  PSG na Parc des Princes 'yan sandan Paris sun kwashe dukkan motocin da ke yankin tare da kafa shingayen bincike a harabar yankin.

Karin bayani: Labarin Wasanni: Yadda ta kaya a gasar olympics bana 

PSG za ka hadu da Barcelona a wasan cin kofin nahiyar Turai a wannan rana ta laraba a wasan dab da kusa da na karshe da miliyoyin mutane za su kalla a duniya. Spain da Burtaniya suma sun tsaurara tsaro tun daga sanarwar kai hari daga kungiyar IS a filayen wasan kasashen Turai har da barazanar amfani da jirage marasa matuka.

Karin bayani: Bayern Munich ta lashe kofin zakarun Turai 

A wasannin da aka fafata a ranar 9 ga watan Afrilu 2024, tsakanin Arsenal da Bayern Munich a birnin Landon na kasar Burtaniya da kuma wasan Real Madrid da Manchester City a Madrid na Span an kammala wasan ba tare da wata matsala ba.