'Yan ta'adda sun kashe sojoji Nijar 23 a yakin Tillaberi
March 22, 2024Gwamnatin mulkin sojan Nijar ta sanar da mutuwar dakarunta 23 a kwantan bauna da masu ikirarin jihadi suka kai a yankin da ke kusa da iyakar kasar da Burkina Faso da Mali. Wannan sabon harin ya faru ne a lokacin da sojojin ke sintiri a cikin wannan mako don dakile ayyukan ta'addanci a yankin Tillabéri, wanda ya ba su damar kame 'yan ta'adda kusan talatin, a cewar sanarwar da ma'aikatar tsaro ta fitar a birnin Yamai.
karin bayani:Matsalolin tsaro bayan juyin mulki a Nijar
Tun shekarun bakwai da suke gabata ne yankin Tillabery ya zama maboyar masu ikirarin jihadi ciki har da Al Qaeda, inda ake fama da hare-haren kungiyoyi da ke dauke da makamai, duk da dimbin dakarun da ke jibge a wannan yanki. Ko da a karshen watan Janairu, an kashe fararen hula 22 a wani hari da aka kai a kauyen Motogatta da ke cikin gundumar Tondikiwindi mai nisan kimanin kilomita dari da babban birni Yamai.
Karin bayani: Rundunar tsaron hadin gwiwa a kasashen AES
Tun a karshen watan Yulin 2023 ne, Jamhuriyar Nijar ta koma karkashin jagorancin sojoji da suka karbe mulki domin a cewarsu su dakile tashe-tashen hankulan da 'yan ta'adda ke haddasawa, amma ana ci gaba da kai hare-hare nan da can.