Nijar: Juyin mulki da matsalolin tsaro
October 17, 2023Duk da matakan da hukumomin sojan Jamhuriyar ta Nijar ke ikirarin dauka a fannin tsaron 'yan ta'addar na ci gaba da zafafa kai hare-hare musamman kan jami'an tsaro bayan juyin mulkin da sojoji suka yi, inda suka halaka sama da 200 a kasa da watannin uku. Hari na baya-bayan nan wanda Nijar din ta fuskanta shi ne wanda 'yan ta'addan suka kai kauyen Tagey na jihar Tera cikin Jihar Tillaberi, inda alkalumman gwamnati suka nuna sojoji shida ne suka halaka tare da jikkata wasu 18 kuma sun jikata yayin dauki ba dadin wanda suka ce 'yan ta'adda sama da 30 sun halaka. Wasu alkalumma da ba na gwamnati ba kuwa sun nunar da cewa tun bayan juyin mulkin Nijar ta fuskanci hare-hare 14 kusan duka a cikin jihar Tillaberi, inda sojoji 229 suka halaka wasu sama da 50 suka yi batan dabo.
Wasu bayanai daga yankin Tamou na jihar Tillaberin na cewa 'yan ta'adda sun kori mutanen kauyuka da dama a yankin, inda suka tsere zuwa manyan garuruwan yankin domin samun mafaka. Duk da matakan da hukumomin mulkin sojan Nijar ke ikirarin dauka kan matsalar tsaron, har yanzu tana ci gaba da yin illa ga harkokin Tattalin arzikin kasar a cewar Alhaji Sani Chekaraou shugaban kungiyar manyan 'yan kasuwa masu shiga da kuma fitar da kaya kasashen waje a Nijar. Sai dai wani abin da ke daurekan mutane a yanzu shi ne irin yadda manyan kungiyoyin fafutuka na jihar Tillaberi wadanda a baya suka yi fice wajen bayyana da kai kuka kan matsalar tsaron da yankin nasu ke fuskanta, sun daina cewa uffan kan lamarin tare da barin talakawan yankin na koke-kokensu ta hanyar shafukan sada zumunta.